Accessibility links

Kwanan nan PDP ta fitar da wata sanarwa inda take cewa wai APC na kokarin raba kawunan 'yan Najeriya bisa ga banbancin addini da kabilanci. Ita APC yanzu ta mayarda martani

A wani sako da mai magana da yawun PDP Olise Metuh ya rabawa manema labarai jam'iyyar ta zargi APC da shirin kawo mummunan tashin tashina a zaben 2015 har ma da kawo siyasar tsatsaurin bin addinin Musulunci irin na jam'iyyar 'yanuwa Musulmi ta kasar Masar da Mohammed Morsi ke jagoranta.

Dan kwamitin zartaswa na kasa na jam'iyyar APC Keften Bala Jibril ya yi watsi da zargin. Ya ce idan batun addini ne shi shugaban kasa Jonathan shi ya kawo batun addini a siyasar Najeriya sabili da baya fadan muhimman batutuwa sai ya je coci ranar Lahadi. A coci yake bada labarai yake kuma fasa kwai na gwamnati da abun da gwamnati take niyar yi. Obasanjo ya yi shugabanci a Najeriya kuma kodayake Kirista ne ba yi wannan ba. Janaral Yakubu Gowon Kirista ne ya yi shugaban kasa amma ba yi haka ba sai shi Jonathan. Ya ce jam'iyyar PDP ta rasa abun da zata yi ko abun da zata kama shi ya sa take neman kwatanta APC da jam'iyyar 'yanuwa Musulmai ta kasar Masar. Babu abun da ba zasu fada ba amma shure-shure ba ya hana mutuwa.

Sai dai wasu 'yan jam'iyyar PDP da suka sha alwashin ko yaya ta kaya ba zasu bar jam'iyyar ba suna ganin mayarda kakkausan lafazi ba zai haifawa jam'iyyarsu da mai ido ba. Abdulrazak Zaki yana cewa idan PDP bata gaggauta yin gyara ba to za'a ruguzar da jam'iyyar kuma zasu nitse. Jam'iyya ta kama hanyar rugujewa amma idan Allah ya so aka gaggauta gyara sai a yi gudu tare a kuma tsira tare. Shi kuma karamin ministan kudi Yarima Ngama ya yiwa APC zagin kasuwa. Ya ce APC bata warkar da ciwon kai sai dai ta saka hauka. Idan ana son warkaswa sai PDP.

Ga karin bayani,

XS
SM
MD
LG