Masari Ya Yi Bayani Kan Ceto Daliban Kankara

Daliban Da Aka Sace.

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya bayyana cewa gwamnati za ta bincike lafiyar daliban makararantar sakandaren Kankara da mahara su ka yi garkuwa da su a daren Jumma'a.

A cikin hirar shi da Muryar Amurka, gwamna Masari ya bayyana cewa, an sami ceto daliban baki daya ba tare da zubda jini ba. Yace bayan da gwamnati ta sami nasarar ceto daliban ta tura motoci tare da jami'an tsaro a jejin da aka tara su domin a dawo da su Katsina.

Gwamna Masari ya ce bayan sun iso katsina kwararrun likitoci da aka ajiye su tarbe su, zasu duba lafiyarsu kafin a mika su ga iyayen su. Ya kuma bayyana cewa tuni aka sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya ke ziyara a Daura a halin yanzu, kuma zai gana da daliban da safe kafin ya koma Abuja.

an-kubutar-da-dalibai-340-da-yan-bindiga-suka-sace-a-katsina

yadda-daya-daga-cikin-daliban-da-aka-sace-a-katsina-ya-kubuta

daliban-sakandaren-kankara-yadda-aka-yi-na-kubuta

Daliban Da Aka Sace

Dangane da batun wani yaro da aka ce ya kira iyayen shi ya shaida masu cewa suna dokar daji amma basu san yadda zasu yi su koma gida ba, gwamnan ya ce ba shi da wannan labarin sai dai idan haka ta ke, ya zama da sauki domin za a iya amfani da wayar shi wajen gano inda su ke a iya ceto su.

Saurari cikakken bayanin gwamnan a hirar shi a wakilin Sashen Hausa Sani Shu'aibu Malumfashi.

Your browser doesn’t support HTML5

Hira da gwamna Aminu Bello Masari kan ceto daliban Kankara:1:30"

Your browser doesn’t support HTML5

Shugaba Muhammadu Buhari Yana Ganawa Da Daliban Kankara Da Aka Saki

Karin bayani akan: Boko Haram, sojoji, Buhari, da jihar Katsina.