Mazauna Ibadan Sun Koka Akan Tsaro a Arewa

Mutane sunyi dafifi kewaye da inda boma-bomai suka tashi a Maiduguri, ranar 14 ga watan Maris 2014.

Dangane da tarzoma da rashin tsaro dake faruwa a arewa maso gabashin Najeriya, Muryar Amurka ta neme jin ra’ayoyin wasu yan arewacin najeriya mazauna kudu maso yammacin Najeriya, musamman ma birnin Ibadan.
Alhaji Yusuf Abubakar Magayakin sarkin sasa, Dr. Haruna Maiyasin Katsina, yace “abubuwa dake faruwa sai dai ace inna liLlahi waina ilaihi rajiun, domin abun bakin ciki ne saboda haka ‘yan uwa musulmi da wadanda ba musulmi ba mu taru mu yiwa kasa addu’a, Allah dai Ya kawo saukin abubuwa dake faruwa a Maiduguri, Yobe, Adamawa da sauran sassan Najeriya.

Alhaji Abubakar yace addu’a fa itace mafutar wanna alamari domin Allah shi yasan wadan da ke tafka wannan tashin-tashina.

Shi kuma zannan Barebari, Alhaji Babagana Kyari kira yayi ga jama’ar arewa maso gabashin Najeriya da ayi hakuri da juna, shima kuma cewa yayi "a dukufa rokon Allah domin samun saukin alamarin."

Your browser doesn’t support HTML5

Mazauna Ibadan Sun Koka Akan Tsaro A Arewa -3'24"