Modu Sherif Ya Zama Shugaban Jam’iyyar PDP Ta Najeriya

Jam'iyyar PDP ta Nigeria

Jami’an Majalisar Koli ta Jam’iyyar PDP sun share wuni guda domin zaben shugaban jam’iyyar daga Arewa maso Gabas, inda daga karshe tsohon gwamnan Borno Ali Modu Sherif, ya zamanto shugaban Jam’iyyar.

Wasu yan Jam’iyyar tun farko sun nuna dari-darin zaman Sharif a matsayin wanda zai maye gurbin tsohon shugaban jam’iyyar Ahmed Mu’azu, wanda yayi murabus tun bayan faduwar babban zabe da jam’iyyar tayi bara.

A cewar wani Jami’in jam’iyyar daga jihar Kaduna, Sa’idu Usman, yace jam’iyyar PDP na bukatar mutane masu martaba da zasu dawo da martabar jam’iyyar. Ya kuma kara da cewa Sherif bai yi dadewar da za a ce an bashi wannan mukami ba.

Sai dai kuma jigogin Jam’iyyar irin su Musa Iliyasu Kwankwaso, sunce basu da ja kan wannan tunda jam’iyya ce ta zaba.

Sherif dai ya fice daga APC zuwa PDP gabanin babban zaben Najeriya a shekarar da ta wuce, wanda shugaba Buhari ya lashe, kwanan nan ma akayi rade radin zai sake dawowa APC amma gashi yanzu ya zama shugaban babbar jam’iyyar adawa ta Najeriya PDP.

Domin karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Modu Sherif Ya Zama Shugaban Jam’iyyar PDP Ta Najeriya - 1'36"