Nijer Ta Bukaci Hadin Kan Jakadun kasashen waje Don Shirin Zaben Ta

CENI - Niger

Hukumar Zaben Jamhuriyar Nijer Ta Bayyana Shirin Fara Rajistar Sunayen ‘Yan Kasar Mazauna Kasashen Waje A Zaben shekarar 2021. da nufin tantance wadanda suka cancanci kada kuri’a a zabubukan 2020 da 2021.

Mahimmancin kuri’un ‘yan Nijer mazauna kasashen ketare a zabubukan kasar, daga na ‘yan majlisar dokoki zuwa na shugaban kasa ya sa hukumar zabe wato CENI soma hangen rajistar wannan rukunin na ‘yan Nijer kamar yadda dokokin zaben kasar suka wajabta a basu damar morar wannan ‘yanci dake rubuce cikin kundin tsarin mulkin kasar wato, inji shugaban hukumar ta CENI Malam Issaka Souna.

Bukatar samun sassauci wajen tafiyar da wannan aiki daga wajen hukumomin kasashen da abin ya shafa ta sa hukumar zaben Nijer kiran taro domin gabatarwa jakadu wannan bukata kamar yadda kakakin hukumar ta CENI Malam Nafiou Wada ke karin bayani akai.

Gwamnatin jamhuriyar Nijer, a ta bakin karamar ministar harakokin waje Madame Salamatou Bala Goga, ta tunatar da jami’an diflomasiyyar dake jakadanci a wannan kasa cewa yana da kyau su dafawa hukumar ta CENI don ganin aikin rajistar ya kammala kamar yadda ake bukata.

Koda yake hukumomin Nijer na ikirarin daukar dawainiyar kudaden da ake bukata don gudanar da zabubukan na 2020 da 2021 hukumar ta CENI ta yi kira ga kasashe aminnan ta da kungiyoyin kasa da kasa da su tallafa da dukkan abinda ya sauwaka.

Ga karin bayani cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Taron Hukumar Zabe Da Jakadu A Jamhuriyar Nijar 2'19