Senegal Ta Kai Zagayen Wasan Karshe A Gasar AFCON

'Yan wasan Senegal suna murna

Yanzu Senegal za ta jira wanda zai yi a nasara tsakanin Egypt da Kamaru a wasan semi finals na biyu da za a buga a ranar Alhamis.

Senegal ta kai wasan karshe bayan da ta doke Burkina Faso da ci 3-1 a zagayen semi finals a gasar cin kofin nahiyar Afirka.

Wannan shi ne karo na biyu a jere da Senegal take kai wa wasan karshe a gasar ta Afcon.

Yanzu Senegal za ta jira wanda zai yi a nasara tsakanin Egypt da Kamaru a wasan semi finals na biyu da za a buga a ranar Alhamis.

Dan wasan Senegal Diallo ne ya fara zura kwallo a minti na 70 sai Gueye ya kara wata kwallon a minti na 76.

Dan wasan Burkina Faso Toure ne ya farke kwallo daya a minti na 82.

Daga bisani kuma Sadio Mane ya kara wata kwallon a minti na 87.

An dai kwashe daukacin zagayen farko na wasan ba tare da an ci kwallo ba, sai bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci kwallayen suka fara samuwa a wasan.

Yanzu Burkina Faso za ta jira wanda ya sha kaye a tsakanin Kamaru da Egypt don neman matsayi na uku.