Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tunisia Ta Yi Waje Da Najeriya A Gasar AFCON


'Yan wasan Tunisia a gasar AFCON
'Yan wasan Tunisia a gasar AFCON

Ana minti na 66 ne kuma aka ba Alex Iwobi jan kati saboda wata shigar keta da alkalin wasan ya ce ya yi wa dan wasan Tunisia.

‘Yan wasan Tunisia sun kai zagayen quarter-final a gasar cin kofin kasashen nahiyar Afirka ta AFCON bayan da suka doke Najeriya da ci daya mai ban-haushi.

‘Yan wasan Carthage Eagles sun zura kwallonsu ne ta hannun dan wasanu Msakni a minti na 47.

Ana minti na 66 ne kuma aka ba Alex Iwobi jan kati saboda wata shigar keta da alkalin wasan ya ce ya yi wa dan wasan Tunisia.

Hakan ya sa kasa lissafin Najeriya ya kara dagulewa, kuma a haka ta karasa wasan da ‘yan wasan goma.

Yanzu Tunisia ta zama kasa ta biyu da ta kai zagayen quarter-final bayan Burkina Faso da ta doke Gabon.

Ita dai Tunisia ta fuskanci kalubale da dama a wannan gasa ta AFCON 2021, a wasanta na farko ta sha kaye da 1-0 a hannun Mali kafin ita ma ta yi wa Mauritania cin kaca da ci 4-1 a wasanta na biyu.

‘Yan wasan Agustine Eguavoen na Super Eagles sun doke Egypt da ci 1-0, Sudan 3-1 da Guinea-Bissau da ci 2-0 a rukunin D.

Masu sharhi da dama sun yi hasashen Najeriya na daya daga cikin kasashen da ake hangen za su iya lashe kofin, lura da irin rawar da ta taka a zagayen rukuni.

A Kididdigar watan Disambar 2021 da FIFA ta yi, Tunisia na matsayi na 30 a iya taka kwallo a duniya yayin da Najeriya take matsayi na 36

Gabanin wasan na Najeriya da Tunisia, Burkina Faso ta doke Gabon da ci 7-6 a bugun fenariti, lamarin da ya ba ta damar shiga zagayen na quarter-final.

Bangarorin biyu sun kai ga matakin bugun fenaritin ne bayan da aka tashi da ci 1-1 a wasan wanda aka buga a filin wasa na Limbe.

Burkina Faso ita ce kasa ta farko da ta fara kai wa ga zagayen na quarter-final.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG