Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

AFCON 2022: Yadda Buga Kwata Final Zai Kasance Na Wasan Gasan Cin Kofin Afirka


A jiya Laraba ne aka buga wasannin ƙarshen zagaye na biyu na gasar cin kofin Afirka dake gudana a kasar Kamaru. Equatorial Guinea tayi nasara kan Mali, inda Misra kuma ta doke Ivory Coast. Duk wasanin biyu a fanareti bayan ƙarin lokaci suka rarraba.

Wannan shine karo na tara cikin karawa 10 da Masar ta doke Ivory Coast a gasar cin kofin nahiyar Afirka. Fitaccen dan wasa Masar Mohamed Salah ne ya zura ƙwallon ƙarshe, da ya bai wa ƙasanshi damar zuwa zagaye na gaba a bugun daga kai sai mai tsaron gida. Karo na uku kenan da "Giwayen Ivory Coast" suke rashin nasara a bugun fanariti da Masar, bayan wasan karshe na 2006 da kuma na kusa da na karshe a 1998.

Wasan da aka yi tsakanin Mali da Equatorial Guinea shi ma ya kasance cikin shakku. Har ƙarshen lokacin ƙa'ida, ƙasashen biyu suna kunnen doki 0-0. A ƙarshe Équatorial Guinea ta yi nasara a bugun fenariti (6 da 5).

Da haka ne Equatorial Guinea za ta fafata da Senegal a wasan kwata fainal ranar Lahadi mai zuwa. A yayin da Masar kuma zata kara da Morocco. Dukan su a Yaounde.

Kafin wa'annan wasani, za'a kara ranar Asabar a Garoua tsakanin Burkina Faso da Tunisiya. Haka kuma Kamaru mai saukan baƙi za ta fafata da Gambiya a birnin Douala.

Za a buga wasan kusa da na karshe ne a ranakun 2 da 3 ga watan Fabrairu, inda za a yi wasan karshe kuma a ranar 6 ga watan Fabrairu.

Saurari rahoto cikin sauti daga Mohamed Ladan:

AFCON 2022: Yadda Buga Kwata Final Zai Kasance Na Wasan Gasan Cin Kofin Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:09 0:00


Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG