Sheikh Dahiru Bauchi Yace Babu Wata Hujja ta Kin Karbar Maganin Rigakafin Polio

Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Shaihin malamin yace ya kamata a kawar da mugun tunani a kyale yara su samu maganin rigakafin wannan muguwar cuta
Kiran da a karbi maganin rigakafin cutar shan inna ko Polio hannu bibbiyu, yana kara samun amo daga wurin manyan shaihunan malamai na Najeriya.

Sheikh Dahiru Usman Bauchi, yana daga cikin manyan malaman addinin Isdlama da suka fito da kakkausar harshe su na fadin cewa babu wata hujja ta kin karbar wannan maganin rigakafi.

Sheikh Dahiru yace ya kamata mutane su rika tunani cikin basira, domin hukumomin kiwon lafiya na duniya sun yi amfani da irin wannan matakin suka kawar da cututtuka da dama wadanda suka addabi jama'a a can baya, kamar agana da ciwon barci na kudar tsando.

Yace akasarin mata a asibiti suke haihuwa, ko suke zuwa awu ko suke zuwa neman magani idan ba su da lafiya, kamar yadda su mamazajen suke zuwa asibiti neman magani. Yace idan har ba a sanyawa mutum wani abu a can ba, mai diga maganin rigakafi ma yara kanana ne zai sanya musu?

Shaihin malamin ya bayar da hujjoji da dama na addini da suka halalta yin rigakafi, ya kuma ce wajibi ne ga iyaye su ba 'ya'yansu maganin rigakafin nan.

Your browser doesn’t support HTML5

A Kawar Da Gurguwar Fahimta Kan Polio In Ji Maulana Sheikh Dahiru Bauchi - 3'07"