Accessibility links

Yara Miliyan Daya Ake Kokarin ba Maganin Rigakafin Polio Yanzu Haka a Anambra


Kwamishinan lafiya na jihar Anambra, Dr. Lawrence Ikeakor, yace duk da cewa ba a samu rahoton Polio ko guda daya a jihar ba, ba zasu yi sakaci har cutar ta sake bullowa ba.

Gwamnatin Jihar Anambra a kudancin Najeriya ta ce yara miliyan daya ne ta ke da niyyar samarwa da maganin rigakafin kamuwa da cutar shan inna ta Polio a wannan zagaye na aikin rigakafin da aka kaddamar asabar, kuma za a kammala gobe talata.

Kwamishinan lafiya na jihar Anambra, Dr. Lawrence Ikeakor, yace duk da cewa ba a samu rahoton Polio ko guda daya a jihar ba, ba zasu yi sakaci har cutar ta sake bullowa ba.

Yace babban gurinsu shi ne kara karfafa amincewa da maganin da ake digawa don rigakafin Polio, OPV, da kuma rage bullar cututtukan da ake iya yin rigakafinsu. Yace wani gurin kuma shi ne na tabbatar da kawar da Polio kwata-kwata a jihar da kuma Najeriya baki daya.

Dr. Ikeakor yace zasu tabbatar da cewa kowane yaron da ya cancanta a jihar ya samu digo biyu na maganin rigakafin Polio, kuma za a bi gida gida, coci-coci, masallatai, makarantu, tasoshin mota, kasuwanni, da kuma dukkan asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya dake jihar, domin bayar da wannan maganin.
XS
SM
MD
LG