Shugaba Muhammad Buhari Yayi Ma Majalisar Zartaswarsa Bayanin Zuwansa Amurka

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya yayi amfani da taron mako-mako na majalisar zartaswar kasa wajen bayyanawa ministocinsa yadda tattaunawarsa da shugaba Donald Trump ta Amurka ta kasance, da kuma irin hidimomin da ya gudanar a Majalisar Dinkin Duniya.

Kakakin shugaban na Najeriya, Malam Garba Shehu, ya fadawa wakilin Muryar Amurka, Umar Faruq Musa, cewa shugaban ya yaba da alkawarin da shugaba Donald Trump ya yi masa cewa Amurka zata saidawa da Najeriya jiragen yakin sama na kai farmaki samfurin Super-Tucano, domin yakar 'yan Boko Haram.

Kakakin yace, shugaba Buhari ya lura cewa a can baya, Amurka ta ki yarda ta saidawa da Najeriya wadannan jiragen.

Haka kuma, majalisar zartaswar ta bayyana damuwa a kan yawan kungiyoyi da hukumomi na kasa da kasa da Najeriya ta shiga ciki, wadanda kuma ba ta cin moriyar komai daga wasunsu. A dalilin haka, majalisar ta yanke shawarar cewa daga yanzu, sai kungiyoyin da shugaban kasa ya zaba da kansa kawai Najeriya zata nemi wakilci cikinsu.

Ga cikakken rahoto da hirar da Umar Faruq Musa yayi da Malam Garba Shehu.

Your browser doesn’t support HTML5

Shugaba Buhari Yayi Bayanin Ganawarsaa Da Shugaba Trump Da Jawabinsa A MDD