Shugaba Trump Ya Jinjinawa Yarima Bin Salman

Donald Trump da Yarima Mohammed bin Salman

Trump ya fada a yau Asabar cewa ya ji dadin yanda Yarimar ya sayi kayan aikin sojoji daga Amurka, ya kuma ce Yarimar ya taka rawar gani wurin kawo sauye sauyen tattalin arziki da harkokin jama’a a kasarsa.

Shugaban na Amurka yaki amsa tambayoyi da ‘yan jarida suka masa ko zai tabo batun mutuwar dan jaridar nan na Saudi Arabia Jamal Kashoggi da ya faru a bara. Yarimar Saudiya dai ya sha sukar kasashen waje a kan kashe Kashoggi, kisar da aka aikata a ofishin jakadancin Saudiya a Istanbul a bara.

Bayan wata liyafar karin kumallo da safiyar yau Asabar, fadar White House tace shugabannin biyu sun samu tattaunawa mai amfani, sun tattauna batun yawan barazana daga Iran da batun inganta kasuwar mai ta duniya da kuma wasu muhimman batutuwan kare ‘yancin bil adama.