Shugaba Trump Ya Mayarwa Jakadan Birtaniya A Amurka Da Martani

Shugaba Trump

A jiya litinin ne Shugaban Amurka Donald Trump, ya ce ba zai kara ma'amala da jakadan Burtaniya a Amurka ba, bayan da jakadan ya kwatanta Trump din da "dakiki," "matsorace," kuma "marar kwarewa," sannan gwamnatinsa kuma "rikitacciyar da babu kamarta."

"Ni ban ma san wannan Jakadan ba," abin da Trump ya fada kenan game da jakada Kim Darroch. Ya kara da cewa, "to amma ba a ma son shi, ko kulawa da shi a cikin Amurka."

Yayin da muryar Amurka ta tambayi fadar white house ko sun rubuta wa offishin jakadancin Burtaniya wasikar martani, sai fadar da White House ta ce a tuntubi Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka, wadda ita kuma ta ce a koma ga fadar ta White House.

A halin da ake ciki kuma, kasar Burtaniya na ta fadi tashin gano wanda ya kwarmata wadannan sakonnin harkokin diflomasiyya na Darroch kama daga Washington zuwa kasarsa, Ingila.