Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Girgizar Kasa Ta Afkawa Kudancin Jihar California


Da safiyar jiya Alhamis ne aka samu girgizar kasa mai girman maki 6.4 a kudancin jihar California, lamarin da ya haifarwa dubban gidaje a yankin rasa wutar lantarki har ma da gobara.

Girgirzar kasa mai karfin maki 6.4 ta afkawa kudancin jihar California da safiyar jiya Alhamis, inda ta girgiza mazauna yankin tare da haddasa gobara da yawa da kuma haifar da barna a garin Ridgecrest, dake da tazarar kilomita 180 daga arewa maso gabashin birnin Los Angeles. Ana kuma ci gaba da fuskantar wasu birbidin girgizar kasa.

Dubban mutane sun rasa wutar lantarki a kusa da inda girgizar kasar ta fi karfi, bayan da ta fara da missalin karfe 10 da rabi da minti uku agogon yankin, kuma wani gida ya kone kurmus.

Shugaban ‘yan kwana-kwana na karamar hukumar Kern, David Witt, ya fadawa manema labarai cewa “Mun samu mutanen da suka ji rauni da yawa, kuma an sami gidaje biyu sun kama da wuta. Haka kuma mun sami wata karamar wutar daji, falwayoyin wuta sun fadi, sai kuma fashewar iskar gas da aka samu, dukkansu akan samesu ne bayan an sami babbar girgizar ‘kasa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG