Shugabannin Siyasa Dana Soji Sun Nada Micheal Kafando a Matsayin Shugaban Kasa

Tsohon Ministan harkokin wajen kasar Burkina Faso Michel Kafando.

Hukumomi a kasar Burkina Faso sun nada tsohon Ministan harkokin wajen kasar Michel Kafando a matsayin shugaban kasa na wucin gadi, kuma an dora masa alhakin jagorancin kafa gwamnatin farar hula.

Kwamitin daya kunshi yan siyasa da sojoji da shugabanin addinai dana kungiyoyin jama'a ne ya bada sanarwa zaban Mr Kafando a yau litinin kwana daya bayan an fara yin shawarwari nada shugaban.

Shugaban masu hamaiya Zephirin Diabre ya baiyana zaban Mr Kafando a zaman na yi da wajewa.

Mataki na gaba shine Mr Kafando zai nada Prime Minista wanda shi kuma zai kafa gwamnatin wucin gadi.

A yayinda yake zantawa da yan jarida a yau Litinin sabon shugaban yace gwamnatinsa zata yi aikin samun nasarar kafa gwamnatin farar hula.