Sojojin Chadi Sun Kwato Garin Malam Fatori na Jihar Borno Daga Hannun 'Yan Boko Haram

Sojojin Chadi na kare iyakar Najeriya. (File Photo)

Sojojin Chadi sun kwato garin Malumfatori dake dab da tabkin Chadi a cikin Jihar Bornon Najeriya, kuma a dab da bakin iyakar Najeriya da kasar Nijar.

Sojojin Chadi sun kwato garin Malumfatori dake dab da tabkin Chadi a cikin Jihar Bornon Najeriya, kuma a dab da bakin iyakar Najeriya da kasar Nijar.

Wani mutumi a garin Bosso dake tsallaken iyaka a cikin Jamhuriyar Nijar, ya fadawa VOA cewa tun jiya suke ganin jiragen saman yaki su na shawagi zuwa garin na Malumfatori, inda suka yi ta jin karar bama-bamai.

Yace a yau alhamis su dake garin Bosso suka samu labarin cewa a yanzu sojojin Chadi ne ke rike da garin na Malumfatori.

An girka sojojin Nijar a bakin iyaka domin hana mayakan Boko Haram dake gudu tsallakawa cikin Nijar.

Da ma dai akasarin mazauna garin na Malumfatori sun riga sun gudu tun bayan da 'yan Boko Haram suka kama shi.

Har yanzu ba a ji ta bakin hukumomin Najeriya kan wannan labarin ba.