Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Boko Haram Sun Kone Michika da Kauyukan dake Kewaye da Garin Kurmus


Shugaban 'yan Boko Haram.

Bayan da suka kone garin Michika 'yan kungiyar Boko Haram sun kai farmaki a kauyukan dake kewaye da garin wadanda tayi rugu-rugu dasu

Kawo yanzu dai ba'a san adadin mutanen da kungiyar ta kashe ba.

Babu abun da 'yan kungiyar Boko Haram suka bari kama daga mutane zuwa gidaje da dabbobi, kai har ma da itatuwa.

Mr Adamu Kamale mai wakiltar yankin a majalisar dokokin jihar Adamawa ya bukaci a kai masu doki. Ya lissafa kauyukan da aka kone kuma ya kara da cewa fiye da kashi hamsin na al'ummar yankin sun yi asarar rayukansu. Ya kira gwamnati ta tura dakarunta domin kwato yankin daga hannun 'yan Boko Haram da kuma kawo karshen kashe-kashe da ake yi.

Har yanzu jami'an tsaro basu ce uffan ba akan hare-haren da aka cigaba da kaiwa yankin. To saidai kungiyar maharba da 'yan kato da gora sun ce suna kokarin kwato yankin. Sun bukaci gwamnatocin Borno da Yobe su fito su bada tasu gudunmawar.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:11 0:00

Bidiyo

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwarya A Mali Goita Ya Tsallake Rijiya Da Baya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Sanarwar Neman Afuwa daga Malam Abdujabbar Kabara
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Yi Tattaki Gida Bayan Ya Idar Da Sallar Eid El-Kabir a Daura
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:06 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Zauren VOA: Najeriya da Kaubalen 'Yan Aware - 005
please wait

No media source currently available

0:00 0:22:55 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Matsalar Tsangwamar Mata Masu Saka Abaya A Kanon Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG