Sun Dauka na Mutu Suka Jefar Da Ni A Cikin Jeji

irin matasan da ke shiga kungiyar Boko haram wadanda yawancin su ke fadawa hannun jami'an tsaro

Babu alamun aikin Allah a Boko Haram, inji dan kungiyar da ya kubuta, ya ce sai kisa da kwacen dukiyar jama'a
Wani matashi dan shekara ishirin da biyu da haihuwa ya tona asirin kungiyar Boko Haram. Matashin dan Boko Haram ne wanda jami’an tsaro suka tsinta jina-jina a jeji a yashe bayan wani harin da suka kai garin Damboa, a tazarar kimanin kilomita tamanin da bakwai da Maiduguri, jahar Borno. Bayan ya koma cikin hayyacin shi ya yiwa kungiyar ta Boko Haram fallasa da tonon sililin cewa jihadin da kungiyar ke ikirarin yi karya ta ke yi, ba jihadin da take yi illa ci da addini, ya ce ba abun da ‘yan kungiyar ke aikatawa sai kashe-kashen keta da azabtar da al'umma da kwace musu dukiya. Wakilin Sashen Hausa a jahar Borno, Haruna Dauda Biu ya yiwa matashin tambayoyin da ya fara yi kamar haka:

Your browser doesn’t support HTML5

dan boko haram na tona asirin kungiyar - 5:51