Accessibility links

Jiya jumma'a ne rundunar sojoji dake gudanar da ayyukan tsaro ta ce kada kowa ya fito waje yayin da take kokarin kakkabe 'yan ta'addar da suka kai farmaki a Damaturu

A yau aka shiga rana ta biyu da kafa dokar hana fita waje kwata-kwata a Jihar Yobe, a bayan farmakin da wasu 'yan bindigar da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne suka kai cikin Damaturu, babban birnin Jihar a daren alhamis.

An bayyana cewa komai tsit, yayin da al'amuran na yau da kullum suka tsaya cik a Damaturu da sauran sassan jihar a sanadin wannan dokar hana yawo.

Motocin 'yan kasuwa da suka saba bi ta cikin Jihar Yobe a tsakanin Maiduguri da Kano, sun kasa wucewa, inda wadanda suka fito daga Kano yawancinsu suka tsaya a Azare a Jihar Bauchi a saboda hana zirga-zirga a cikin jihar ta Yobe.

A jiya jumma'a ne kakakin Bataliyar Zaratan Sojojin Najeriya ta shiyya ta 3, Kyaftin Eli Lazarus, ya bayarda sanarwar kafa wannan dokar hana fita waje, inda yace an fara aiki da wannan doka tun daga lokacin.

Kyaftin Lazarus ya roki jama'a masu bin doka da oda da su kwantar da hankulansu a yayin da bataliyar take ci gaba da kokarin kawar da 'yan bindiga daga wuraren da suka yi tunga.

Jihar Yobe tana daya daga cikin jihohi ukun da aka kafa dokar-ta-baci a yunkurin kawo karshen cin kare babu babbaka da kungiyar Boko Haram take yi a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
XS
SM
MD
LG