Tsohon madugun 'yan tawayen Biyafara, Ojukwu, ya mutu a Burtaniya

  • Ibrahim Garba

Marigayi Odumegwu Ojukwu

Wani tsohon kanar din sojin Nijeriya, dan siyasa kuma shugaban tsohuwar

Wani tsohon kanar din sojin Nijeriya, dan siyasa kuma shugaban tsohuwar ballalliyar janhuriyar Biafara, ya mutu yana da shekaru 78 a duniya.

Chukwuemeke Odumegwu Ojukwu, ya mutu a wani asibitin London, bayan wata doguwar jinyar da ta biyo bayan hawan jinin da ya samu.

Ofishin shugaban Nigeria Goodluck Jonathan, ya bayar da sanarwa a jiya Asabar cewa, za a rinka tunawa da Ojukwu a matsayin daya daga cikin jaruman lokacinsa, wanda aka sanshi da rashin tsoro, da gaba-gadi da kuma iya bi da mutane.

To amman a matakin kasa da kasa, an fi tunawa da shi ne da hotunan ramammun kananan yara a yankin Biafra.

Dan daya daga cikin wadanda su ka fi dukiya a Nijeriya, kuma wanda ya yi makaranta a Burtaniya, Ojukwu ya yi fice ne a duniya a yayin juyin mulkin Nijeriya na 1966. Kimanin mutane miliyan guda ne su ka mutu a wannan yakin basasan da ya biyo baya.

Wani juyin mulkin da ‘yan arewacin Nijeriya su ka yi wanda ya fi shafar kabilarsa ta Igbo, ya kais hi ga ayyana ‘yancin Janhuriyar Biafra a gabashin Nijeriya a 1967. Duk da samin agaji daga kasashen waje da ya yi, dogaro na tsawon lokaci kan kayan abinci daga wasu yankunan da ke makwabtaka da Biafara, ya janyo matsanacin karancin abinci cikin shekaru uku na biye da aka yi ta yi ana yaki.

Bayan da aka yi galaba kansa a 1970, sai Ojukwu ya tsere daga kasar ya yi shekaru 13 ya na kudin hijira.

Ya dawo Nijeriya bayan da aka masa afuwa a 1982, daga bisani kuma ya shiga takarar shugaban kasa har sau biyu ba tare da nasara ba.

Ana daukarsa a matsayin kwarzo tsakanin mutanensa na Igbo, wadanda ke zargin an danne su a siyasance a kasar.

Aika Sharhinka