Accessibility links

Boko Haram Ta karyata Cewa Mutumin da Aka Kama kakakin ta Ne

  • Aliyu Imam

Jami'an tsaro suke sintiri a birnin Maiduguri.

Kungiyar Boko Haram ta karyata cewa Ali Umar konduga wadda aka fi sani da sunan Usman al-Zawahiri dan kungiyar ne.

Kungiyar Boko Haram ta karyata cewa mutumin da hukumar 'yansandan ciki ta SSS ta kama Ali Umar Konduga, wadda aka fi sani a kafofin yada labarai da sunan Usman al-Zawahiri dan kungiyar ne.

Da yake magana da manema labarai ta woyar tarho a birnin Maiduguri, wani wadda ya kira kansa Mallam Habu Kaka, yace kowa ya san Ali Konduga dan bangar siyasa ne tareda wata kungiuyar bangar da ake kira Ecomog. kuma yace babu yadda za a yi wani ya hada kungiyoyin biyu.

Mallam Habu yace kungiyar su bata da alaka da duk wata jam'iyyar siyasa. Burinsu yace shine kawar da duk wani tafarkin mulki irin na demokuradiyya da salon mulkin kasashen yammaci. A madadinsa su kafa tsarin shari'a.

Kakakin kungiyar na Boko Haram yace kan wan nan burin, ko iyayensu ne suka nemi hana su aikin addini zasu gama da shi.

Saurari:

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG