Wata Hajiya Daga Jahar Gombe Ta Gamu Da Ajalin Ta

Wata 'yar jahar Gombe ta rasu a aikin Hajji

Aishatu Tukur daga karamar hukumar Balanga, jahar Gombe ta rasu a Makka garin gudun ceton rai
Allah Ya yiwa wata hajiya daga jahar Gombe rasuwa a Makka. Amirul hajjin jahar Gombe, kuma kakakin majalisar dokokin jahar Inuwa Garba ya yi cikakken bayani ga wakiliyar Sashen Hausa Saadatu Mohamed Fawu, amma kafin nan, Saadatu ta yi tattaki har masaukin mata alhazan jahar Gomben inda ta fara tattaunawa da wata shaidar gani da ido, wadda ta soma da bayyana sunan ta kamar haka:

Your browser doesn’t support HTML5

wata 'yar jahar Gombe ta rasu a Makka - 2:35