Accessibility links

Jami'an Tsaro Sun Hana Amirul Hajj Na Jihar Adamawa Shiga Tashar Jirage Dake Yola

  • Aliyu Imam

Mahajjata A Ka'aba.

Jami'an tsaro sun nemi hana Amirul Hajj na jihar Adamawa Shiga Tashar Jiragen Sama na kasa da kasa dake Yola fadar jihar Adamawa.

Sojoji daga rundunar mayakan sama dake Yola babban birnin jihar Adamawa sun nemi hana Amirul Hajj na jihar na bana, wanda har wayau kwamishina ne a majalisar zartaswar jihar.

Amma daga bisani an sami fahimtar juna, suka kyale Amirul Hajj na bana Dr. Salihu Bakari Girei da tawagarsa suka wuce. Da yake magana akai, Amirul Hajjin yace, kasan idan allurar jami'an tsaron ta motsa wani lokaci yana dan wahala kamin su sassauto.

Tuni aka yi jigilar fiyeda maniyyata dubu daya daga jihar, yayinda takwarorinsu daga jihar Taraba makwabciyar jihar Adamawa suke haramar tashi. Kamar yadda zaku ji karin bayani cikin wannan rahoto da Ibrahim Abdulaziz ya aiko mana.

XS
SM
MD
LG