Yadda 'Yan Bindiga Suka Kashe Kusan Mutane 40 a Karamar Hukumar Giwa

Your browser doesn’t support HTML5

Anyi Jana'izar Mutane 34 Da 'Yan Bindiga Suka Kashe A Shinkafi

Al'umomin garuruwan da 'yan-bindiga su ka kai hari a karamar hukumar Giwa sun ce bayan mutane 38 da aka yi jana'izar su jiya Lahadi har yanzu ana cigaba da neman wasu mutane da ake zaton su ma an kashe su,

Yan bindiga

Da yammacin Asabar ido-na-ganin-ido ne 'yan bindiga akan babura su ka afkawa garuruwan Kauran Fawa, Marke da Riheya dake yankin Idasu a Karamar hukumar Giwa, inda su ka dunga harbin kan mai uwar da wabi sannan su ka kone dukiyoyi.

A cikin hirar shi da Muryar Amurka, Malam Ibrahim Shehu Lawal Giwa daya daga cikin al'umar da aka yi jana'izar wadan da su rasu ya ce har yanzu ana neman wasu gawawwaki. Bisa ga cewarshi, 'yan bindigan sun shiga garuruwan ne a kan babura sama da 100, dauke da manyan makamai suka yi ta bude wuta lamarin da ya hana jami'an tsaro shiga nan da nan. Malla Ibrahim Shehu Lawal ya bayyana cewa, banda wadanda aka yi jana'iza, har yanzu ba a ga wadansu mutane ba, wadanda ake kyautata zaton ko dai 'yan bindigar sun yi garkuwa da su, ko kuma sun kashe su.

Ya kuma shaidawa Muryar Amurka cewa, kashe garin wannan harin 'yan bindigar sun sake shiga wani garin suka kashe basaraken.

ran-dan-adam-ba-a-bakin-komai-yake-ba-a-najeriya-atiku

an-soma-fafatawa-don-dakile-ayukkan-yan-bindiga-a-wasu-yankunan-arewacin-najeriya

wasu-yan-bindiga-sun-kai-hari-a-wani-masallaci-a-arewacin-najeriya-suka-kashe-mutane-16

Tuni kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jahar Kaduna Malam Samuel Aruwan ya fidar da jadawali dauke da sunayen wadan da 'yan-bindigan su ka kashe kamar yadda Ya tabbatar.

'Yan bindiga sun kona gidaje a Jos

Wasu masana harkokin tsaro dai na ganin karancin jami'an tsaro na cikin abubuwan da ke kawo tasgaro game da ya ki da 'yan-bindiga.
Ko a makon jiya sai da 'yan-bindiga su tare hanyar Kaduna-zuwa Zariya har sau biyu inda har su ka kashe daya daga cikin 'yan-majalissar dokokin jahar Kaduna daga yankin.
Saurari cikakken rahoton Isah Lawal Ikara cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Yadda 'Yan Bindiga Suka Kashe Mutane Kusan 40 a Karamar Hukumar Giwa