Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Sun Kashe Dan Majalisar Dokokin Jihar Kaduna


Rilwanu Aminu Gadagau

‘Yan bindiga sun kashe shugaban kwamitin kananan hukumomi da raya karkara na majalisar dokokin jihar Kaduna, Rilwanu Aminu Gadagau mai wakiltar mazabar Giwa ta yamma. 

Rahotannin sun bayyana cewa a daren ranar Litinin ‘yan bindiga suka kashe shi a wani hari da suka kai akan hanyar Kaduna zuwa Zariya, amma sai a safiyar ranar Laraba aka ga gawarsa.

Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Yusuf Ibrahim Zailani, ya bayyana Mutuwar Gadagau a matsayin mai tada hankali. A wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Ibrahim Dahiru Danfulani, Zailani ya bayyana Gadagu a matsayin dan majalisar wakilai mai kwazo, a cewar jaridar Guardian ta Najeriya.

“Wannan abin takaici da bakin ciki ne. Muna juyayin wannan lamari,” a cewar Yusuf Ibrahim Zailani.

Ya kuma yi addu’ar Allah Ta’ala ya baiwa jihar, majalisar dokokinta, da iyalansa hakurin rashin.

Mutuwar Gadagau dai na zuwa ne sa’o’i 24 bayan da hukumar tsaron DSS ta farin kaya ta bayyana damuwa kan yadda ake auna ‘yan majalisa ana kashe su.

XS
SM
MD
LG