'Yan Asalin Niger Delta Mazauna Kasashen Turai Da Amurka Sun Bude Gidan Radiyo

Bincike ya nuna cewa wasu ‘yan asalin yankin niger delta dake zama Amurka da Turai wadanda ke adawa da tsattsauran ra"ayi da bakin ciki da fasa bututun mai da matasan yankin ke cigaba da yi, sun kafa wani sabon gidan rediyo a birnin Newyork na kasar Amurka domin yaki da tsagerancin matasan yankin.

Ta dalilin haka ne wakilin sashen Hausa na muryar Amurka Hassan Maina Kaina ya nemi jin ra'ayoyin jama'a da dama musamman kwararru wadanda suka goge a harkokin sadarwa daga arewacin kasar.

Sai dai kuma ra’ayoyin kwararrun akan wannan sabon gidan rediyo ya banbanta kamar yadda tsohon manajan daraktan gidan rediyo na jihar Kaduna Zubairu Idris Abdulra’uf yace koda da kyakkyawar niyya suka kafa wannan gidan rediyo, tunda bai sami amincewar hukumomi a Najeriya ba haka na nufin an bude gidan rediyon ta barauniyar hanya Kenan.

Ya kara da cewa koda an cimma manufar da aka kafa wannan gidan rediyo, daga karshe zasu karkata akalar shirye shiryen su wajan yada fafutukar yankin na Niger Delta.

Shi kuma tsohon manajan gidan rediyon YBC Ibrahim Bulama Naciya cewa yayi a nasa ra’ayin kafa wannan gidan rediyo abu ne mai matukar amfani domin kuwa zasu sauya tunanin wadannan mutane dake neman tada zaune tsaye, zasu wayar da kawunan jama’ar su da fashe fashen bututun mai ke faruwa a yankunan su.

Haka kuma wani dattijo daya taka rawa wajan sulhu tsakanin matasan yankin da tsohuwar gwamnatin marigayi Umar Musa ‘Yar Adu’a yankin na Niger Delta chief TK Ogboriba yace suna maraba lale da wannan tashar rediyo domin a cewar sa abubuwa da daman a faruwa a wannan yanki kuma jama’ar karkara basu da masaniya akan hakan.

Ga rahoton Hasan Maina Kaina.

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan Asalin Niger Delta Mazauna Kasashen Turai Da Amurka Sun Bude Gidan Radiyo