'Yan Shi'a Na Neman Adalci

Sojojin Najeriya. (File Photo)

Darektan kare al’umma da bincike na hukumar Bani Adama, ya ce su na bin diddikin duk hukumar da ta dace don gano gaskiyar kisan da aka yi wa 'yan kungiyar Shi'a.

Mabiya akidar Shi’a sun yi gangamin nuna rashin jindadinsu sakamakon kashe ‘yan kungiyarsu su talatin da hudu da aka yi, ciki harda mutune uku ‘ya'yan shugaban su na Najeriya Sheik Ibrahim Yakubu Al-Zakzaky a Zaria, bayan cin karo da suka yi da sojoji ranar tunawa da gwagwarmayar Paladinawa, wato ranar Kudus watanni shida da suka wuce.

Kisan da aka yi, ya isa ya sa hukumar kare hakkokin Bani Adama ta Najeriya dake birnin tarayya Abuja ta matsa lamba domin samar da adalchi ga wadanda abun ya shafa, ganin cewa yawanci dalibai ‘yan akidar ne abun ya fi shafa.

Hukumar kare hakkin ‘yan adam tace tana aiki kan korafin. Darektan kare al’umma da bincike na hukumar Malam Abdulrahaman Yakubu, yace suna bin diddikin duk hukumar da ta dace don gano gaskiyar lamarin. Ya kara da cewa zasu tabbata sun samar da adalchi ga wadanda abun ya shafa.

Kungiyar Good House dake kemfe din wanzar da zaman lafiya musamman lokacin zabe, ta dage wajen nuna illolin tarzoma. Tarzoma a Najeriya ka haddasa kone-kone, sai dai wata sa'in jami’an tsaro na amfani da karfi mai yawa wajen tarwatsa mutane kuma hakan ka iya shafar wadanda basu ji ba basu gani ba.

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan Shi'a na Neman Adalchi kan Kisan 'Yan Kungiyarsu - 3'03"