Yanayin Kuncin Rayuwa Na Sa All'umma Tarar Aradu Da Ka-Masana

Karancin kanazir ya kaiga sare itatuwa domin dafa abinci

Masana a Najeriya sun yi ammanar cewa, yanayin kuncin rayuwa da 'yan kasar suka tsinci kansu ciki baya rasa nasaba da abinda ke ingiza su neman yanyoyin saukakawa rayukan su koda suna da wasu illoli.

Wani abu da ke nuna hakan shine ganin yadda ake ta yekuwar hana saran itatuwa barkatai amma har yanzu wasu jama'a sun dogara ga amfani da itatuwan da ake sara a zaman makamashi.

Gwamnatoci da kungiyoyi a Najeriya sun jima suna yekuwa akan muhimmancin dashen itatuwa da hana saransu musamman a jihohin da ke fama da gurgusowar hamada.

Masana dai sun bayyana cewa, Najeriya kasa ce wadda a tsawon shekara ba za'a rasa nau'o'in itatuwa ba, da idan aka dasa su zasu rayu, kuma duk da yake wasu lokuta ana dashen itatuwan amma jama'a na ci gaba da fuskantar matsolin da gurbacewar muhalli ke haifarwa kamar fari, da ambaliyar ruwa, da zaizayar kasa da makamantansu.

A tattare da hakan gwamnatoci na ci gaba tinkaho da cewa suna bayar da muhimmanci ga dashen itatuwa a jihohinsu, kamar yadda gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana a hirar shi da Muryar Amurka.

Lamarin kare muhalli ta hanyar dashen itatuwa a cewar masanan muhalli nauyi ne akan kowa, kuma hakan baya rasa nasaba da wani kawance da kungiyar 'yan jarida ta Najeriya reshen jihar Sakkwato ta yi da gidauniyar Mai Koli da wata cibiyar kula da muhalli ta Afirka wajen daddasa itatuwa a Makarantu 50 a jihar Sakkwato.

Sai dai abin dubawa shine yaya za'a gujewa irin matsalar da masana ke gani ta ana dasa itace amma ana fuskantar matsalolin gurbatar muhalli,

Batun gurbatar muhalli dai batu ne da ya ja hankulan kasashen duniya da dama, wadanda ke ta fafatuka wajen ceto muhallin daga ci gaba da gurbata.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Yanayin Kuncin Rayuwa Na Sa All'umma Tarar Aradu Da Ka-Masana