Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Halin Kuncin Rayuwa Da Boko Haram Ta Jefa Wasu ‘Yan Najeriya


Daruruwan Yan Gudun Hijira Da Tashe Tashen Hankula Ya Raba Da Gidaje A Jihar Taraba.
Daruruwan Yan Gudun Hijira Da Tashe Tashen Hankula Ya Raba Da Gidaje A Jihar Taraba.

Mayakan Boko Haram sun addabi arewa maso gabashin Najeriya sama da shekaru goma, tare da tilastawa mutum miliyan 2 tserewa daga gidajensu, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

Akalla 3,000 sun gudu daga karkara zuwa Kawar Maila, wani sansani a Maiduguri babban birnin jihar Borno.

Bayan tserewa daga masu tayar da kayar bayan, wadannan mutanen da aka raba da muhallansu har yanzu suna fuskantar babban kalubale, da suka hada da faman neman abinci da kiwon lafiya, da hanyar ilimantar da ‘ya ‘yansu, da tunanin makoma mai kyau.

“Rayuwa a nan tana da matukar wahala. Muna shan wahala,” in ji Mohammed Abba, wanda ke da gona a yankin Konduga, kimanin kilomita 25 kudu maso gabashin Maiduguri.

Yanzu shi da matarsa da yaransa biyar suna zaune a cikin wani karamin daki daya.

Ya ce “A lokacin damina, za ku yi mamakin ganin yadda muke jurewa. Wannan dakin ya yi ambaliya kuma ba za mu iya kwana a ciki ba, "inj i shi.

Abba ya kasance “yana kiwon dabbobi yana fatauci. Amma wannan shi ne halin da muke ciki a yau.”

Makwabciyarsa Falmata Abukar, ita ma ta zo daga Konduga tare da mijinta.

“Yaro na ya yi rashin lafiya. Bai bude ido ba har kwana hudu. Ba ya iya gani da idanunsa yanzu,” in ji Falmata tana mai cewa, "idon ba zai gyaru ba."

Zawarawa, galibi tare da yara, suna zaune ne a cikin gidan adana kaya da aka ba su aro - fiye da mutum 180 a cikin dakunan da aka raba da zanin yafawa ko leda, Mata galibi suna zaune tare a tsakiya, suna hira yayin da suke sarrafa masara don yin abincin gargajiya da ake kira Bura-Busko.

Mazauna sansanin, wadanda aka kebesu daga harkokin yau da kullun, suna kokarin neman abin da za su ci.

Gwamnan jihar Babagana Umara Zulum, ya ce suna iya bakin kokarinsu wajen ganin sun mayar da ‘yan gudun hijirar gidajensu.

“’Yan gudun hijirar sun gaji da zama a sansanonin, suna kan yi korafi dare da rana kan irin mawuyacin halin da suke ciki. Ba su da abinci sannan ana cin zarafin ‘ya’yansu, akwai bukatar su koma gidajensu.” In ji Zulum.

Sai dai hakan zai yiwuwa ne kawai idan har an karbo yankunan daga hannun mayakan Boko Haram a cewar gwamnan.

“Da farko sai sun mun tabbatar da tsaro a wurin, ba ma son mu mayar da mutane wuraren da babu tsaro." Zulum ya ce.

XS
SM
MD
LG