Yau Lahadi Za’ayi Zabe A wasu Kananan Hukumomin Jihar Borno

Wata jami'ar zabe taje duba sunan mai zabe.

Sai yau Lahadi za’a gudanar da zaben Gwamna dana ‘yan majalisu, da aka soke jiya a kananan hukumomin Bama, Gala, Ganzai da Goza, hakan ya biyo bayane sakamakon rashin isar kayan zaben cikin lokaci, da aka dangantashi da sake katin zaben gwamna sakamakon cire jam’iyyar Leba cikin takardun kada kuri’ar.

Ga cikakken rahotan.