Za A Janye Dakarun Najeriya Daga Wasu Yankunan Arewa Maso Gabas

Sojojin Najeriya a Sambisa

An gudanar da taron majalisar tsaro ta kasa a Najeriya, inda aka yi nazarin sha'anin tsaro a kasar tare da yanke shawarar fara janye sojoji daga wasu yankunan arewa maso gabashin kasar.

An yi bitar halin da tsaron kasar ke ciki a taron wanda ya gudana karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma daukacin manyan hafsoshin sojin kasar baki daya.

Babban hafsan hafsoshin rundunan sojojin ruwan Najeriya, Vice Admiral Ibok -Ite Ikwe Ibas ya yiwa ‘yan jaridu karin bayani jim kadan bayan kammala taron.

“Ya ce a makwanni biyu kawai da suka gabata Boko Haram sun kai hare hare kimanin 27 a shiyar arewa maso gabashin Najeriya kadai, amma jaruman dakarun mu sun dakile hare haren har ma sun hallaka kwamandodin masu tada kayar bayar”.

Taron majalisar tsaron Najeriyan kazalika ya kuma cimma shawarar fara janye sojoji daga wasu yankunan arewa maso gabashin Najeriya a shekarar 2020 mai kamawa.

Sai dai wasu a cikin dattawan arewa maso gabashin Najeriyar ir sun bayyana fargaban janye sojoji daga wannan shiya.

Ga cikakken rahoton daga Hassan Maina Kaina daga Abuja:

Your browser doesn’t support HTML5

TARON MAJALISAR TSARO TA KASA