Zaben Nijar a Kamaru jam'iyyun hamayya sun rungumi kaddara

Shugaba Issoufou Mahamadou na jam'iyyar PNDS Tarayya

Sakamakon zabukan Nijar da aka yi a sassa daban daban a kasar Kamaru jam'iyyar PNDS ce ta lashesu

Duk sakamakon zabukan na rumfunonin zabe a kasar sun tabbatar da nasarar jam'iyyar PNDS akan sauran jam'iyyun.

Cikin jimillar kuri'u 7880 PNDS ta samu kuri'u 1536 sai kuma jam'iyyar MODEL Lumana da ta samu kuri'u 500. Jam'iyyu 13 suka yayyana sauran kuri'un tsakaninsu.

Shugaban jam'iyyar MODEL Lumana Alhaji Audi yace ya amince da sakamakon zaben.Ya yiwa Allah godiya an yi zaben lami lafiya an kuma gama cikin lumana. Ya yiwa masu goyon bayansu godiya.

Su ma sauran 'yan hamayya sun ce sun rungumi kaddara. Sun ce babu magudi an yi zaben a bayyane.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Zaben Nijar a Kamaru 'jammiyyun hamayya sun rungumi kaddara - 4' 54"