Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Takaitaccen Tarihin Mulki A Jamhuriyar Nijar


Tambarin Jamhuriyar Nijar
Tambarin Jamhuriyar Nijar

Wannan shine karo na 6 da ake shirya babban zabe a Jamhuriyar Nijar, tun bayan da kasar ta tsunduma tafarkin dimokaradiyya a 1991, lokacin da kungiyoyin fafutukar kasar suka kawo karshen mulkin shekaru 16 da Janal Ali Saibou ya gada daga marigayi Janal Seyni Kountché.

Wanna ya farune a washegarin taron muhawarar kasa wanda ya sake daura jamhuriyar Nijar a kan wata sabuwar turba, gwamnatin rikon kwarya a karkashin Fara Minista Shehu Amadou ce ta shirya da Alhaji Mahamane Ousmane na jam’iyyar CDS RAHAMA ya lashe, a shekara ta 1992 a karawar sa da Tandja Mamadou a zagaye na biyu, sai dai sojojin sun kifar da shi bayan wasu shekaru uku kacal.

Janal Ibrahim Baré Maïnassara wanda ya jagoranci gwamnatin rikon kwarya tun a zagayen farko ya bayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaben da ya shirya a 1997, a karkashin jam’iyyar RDP JAMA’A, kafin kwamanda Mallam Wanke yayi masa juyin mulki a ranar 9 ga watan Afirilun 1999.

Bayan wasu yan watanni na rikon kwarya Tandja Mamadou na MNSD NASARA ne ya lashe zabe, abinda ya bashi damar shafe shekaru 5 akan madafun ikon kasar, san nan ya sami wa’adin mulki na biyu wanda a hukumance yake kammala a Disambar 2009, to amma Tandja Mamadou ya shirya zaben raba gardama da nufin samun karin shekaru 3, a cewar sa domin ya kammala ayyukan da ya fara, abin da ya ba kwamanda Salou Djibo damar kawar da shi a watan Fabarairun 2010.

Zaben da aka shirya a watan Maris din 2011 ya ba Issoufou Mahamadou PNDS TARAYYA damar yin nasara. Yanzu kuma bayan kammala wa’adin mulki na shekaru 5, shugaban na fuskantar yan takara kimanin 15 tsofafi da sabon jini wanda kowannen su ke bayyana kyakykyawar aniyar lashe wannan babban zabe da za a yi.

Yan jamhuriyar Nijar mazauna Najeriya sun shirya tsaf don fara kada kuri’a a Abuja, wanda za a gudanar da zaban a ofishin jakadancin Nijar.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:25 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG