Bisa ga yadda jama'a suka shiga damuwa a Najeriya saboda sauyin kudi da babban bankin kasar ya yi wanda ya kawo karancin kudi a hannun jama'a, wasu sun soma tsarin bani gishiri in baka manda, yayin da wasu suka karkafafa amfani da kudin kasashen ketare.
A yau 10 ga watan Fabarairu ne babban bankin Najeriya CBN ta bayyana cewa za a daina amfani da tsoffin takardun kudaden da aka canza na Naira 200, 500 da 1000 lamarin da ya haifar da fargaba a zukatan mutane da dama a kasar ganin irin cunkoso da ake fuskanta a wasu bankunan kasar.
“Amurka ta ce ba ta goyon bayan kowane ‘dan takara a zaben Najeriya. Ta ce ita dai babban muradinta shi ne ta ga an gudanar da ingantaccen zabe, na gaskiya mai cike da adalci, wanda kowa da kowa zai na'am da shi”
Matsalar karancin takardun kudin naira da ake fuskanta a yanzu, biyo bayan samar da sabon tsarin takaita yawo da tsabar kudi, ya tilasta wa da dama daga cikin ‘yan kasuwa sayar da kayayyakinsu a farashi mai rahusa don samun kudin da zasu biya wa kansu bukatu na yau da kullum musamman kayan abinci.
Hukumar kiwon lafiyar al’ummar Jamhuriyar Nijar ta ayyana samun nasarar kawar da cutar makantar kuda wato Onchocercose ko River Blindness daga kasar bayan fafutukar shekaru sama da 40.
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma dan takarar shugaban kasar a zaben bana na Jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya fara gudanar da taron gangaminsa na neman kuri’a a Kano.
“Ana dai zargin sojojin da danne hakkin dan Adam ciki har da zubar da cikin mata fiye da dubu goma da ake zargin Boko Haram sun yi wa Fyade”
Bankuna da wuraren cire kudi sun yi cikar kwari, har ta kai ga masu bukatar dibar kudaden sun koma cacar baki da musayar yawu da kuma baiwa hammata iska.
A cikin shirin na wannan makon, mun duba batun bunkasa harkokin ilimi a yankin Arewacin Najeriya, inda yara kanana da dama ba sa zuwa makaranta ko kuma su na gararamba kan tituna ba tare da samun kulawar da ta dace daga gwamnatoci da kuma iyaye ba.
Da safiyar yau litinin wata Girgizar kasa mai karfin 7.8 a ma'auni ta kashe mutane sama da 2, 300 a kasashen Turkiyya da arewacin Siriya, yayinda aka fara aikin nemo masu rai a cikin baraguzan gine-gine da suka rubta.
Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch, ta ce an samu matsalolin take hakkin dan adam a duniya a cikin shekarar da ta gabata, kamar daga Ukraine, China zuwa Afghanistan, da wasu rahotanni
Najeriya da Nijar na ci gaba da karfafa matakan da za su bada damar gaggauta kammala shirinsu na shimfida layin dogo a aikace daga Jihar Kano a Najeriya zuwa Maradi da zai ratsa ta wasu garuruwan Jihar Katsina a Najeriya.
Yayin da ya rage saura mako uku a soma zabubuka a Najeriya masu saka ido kan zabe daga kasashen ketare na ci gaba da kwarara cikin kasar domin ganin yadda abubuwa masu nasaba da zaben ke gudana.
Sama da ‘yan Najeriya 11,000 daga yankin Neja Delta mai arzikin man fetur ne suka shigar da karar kamfanin Shell SHEL.L a gaban babbar kotun birnin Landan, mataki na baya-bayan nan a shari’ar da za ta sa a ga ko wasu ‘yan kasa na ketare na iya neman hakkinsu.
Ministar kudin Najeriya ta ce a ranar Alhamis din nan ba ta amince da, abin da ta kira, wani abin mamaki, da hukumar Moody’s ta yi na rage darajar kasar game da basussuka ba, tana mai cewa tuni gwamnatin kasar ta magance matsalolin da hukumar ta bayyana.
A cikin shirin na wannan makon mun leka Jihar Maradi a Jamhuriyar Niger inda aka samu bullar wani sabon nau'in cutar Polio.
Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun cafke wasu tsofaffin shugabannin hukumar shigi da ficin kaya a ci gaba da binciken da hukumar yaki da cin hanci ta kaddamar kan wata badakalar da ta shafi dubban miliyon cfa wace ake hasashen za ta iya rutsawa da dimbin jami’an Douane, wato kwastam.
‘Yan takarar kujerar gwamna a jihar Filato sun sha alwashin magance tarin matsalolin da jihar ke fuskanta in har suka samu nasarar lashe zabe.
Dinbin sarakunan gargajiya, malamai da kusoshin gwamnati daga sassan Arewacin Najeriya na cikin dubun dubatar al'umar Musulmi ne suka halarci Sallar jana'izar mai martaba sarkin Dutse, Mai Martaba Alhaji Nuhu Muhammad Sanusi wanda Allah ya yiwa rasuwa a jiya Talata.a babban asibitin kasa dake Abuja.
Domin Kari