Shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya, Rev. Dr. Samson Ayekunle, ya kai ziyar sansanin 'yan gudun hijira na Cocin EYN a unguwar Wulari da ke Maiduguri babban birnin jihar Borno, inda ya ba da tallafi ga 'yan gudun hijirar da ke sansanin.
Bayan da kotun soja da ke zama a Garin Maiduguri, hedikwatar jahar Borno, ta samu sojan sama Flight Lt. Matins Enweran da laifin aika ta fyade ga wata yarinya 'yar shekaru 14 kuma yar gudun hijra da ke zaune a sansanin Bakasi, kotun ta kore shi daga aikin soja tare da rage masa mukami.
Yayin da 'yan jam'iyyar APC ke cigaba da shagulgulan nasarar zabe a jahar Borno, wasu 'yan PDP na ganin da kamar wuya a ce dinbin wadanda su ka yi rajista sun fito sun kada kuri'a kamar sam babu wanda ya mutu ko kuma ya kaura.
A yammacin jiya Litinin da misalin karfe shida ne wasu da ake zaton 'yan boko haram ne suka kai hari a kan jami’an soja a kwauyen Auno dake daf da shiga garin Maiduguri.
Yan gudun hijira daga garin Baga sun koka da irin halin da suke ciki, tun lokacin da suka tsere daga garuruwan su zuwa Manguno da babban birnin jihar Borno, Maiduguri. saboda yadda 'yan Boko Haram su ke kona gine-ginan gwamnati dana manyan mutane a garin.
"Masana a fannin tsaro na ganin an yaudari Shugaba Muhammadu Buhari da ‘yan Najeriya musamman kan yadda a baya aka yi ta cewa an gama da ‘yan Boko Haram saura dan burbushinsu."
Wata arangama tsakanin sojojin Najeriya da mayakan kungiyar Boko Haram ya yi sanadiyar ran wani soja daya tare da raunata wani guda.
Wasu al’ummar jihar Borno sun nuna damuwarsu game da irin hare-haren ta’addanci dake kara ta’azzara akan jami’an tsaro da ma jama’ar da ke kewaye da babban birnin Maiduguri.
An ware kananan yara ‘yan kasa da shekaru 18 daga cikin ‘yan kungiyar sa kai ta Civilean JTF, an kuma mika su ga asusun tallafawa kananan yara na MDD.
Jami’an sojan Najeriya da hadin gwiwar na kasar Chadi sun ce sun hallaka ‘yan kungiyar Boko Haram 124 a wasu hare-hare daban-daban da su ka kai musu.
Da alamu wata sabuwar rigima ce ke kokarin kunno kai a tsakanin ‘ya ‘yan jam’iyyar APC a jihar Borno, sakamakon zaben fidda gwani da aka yi a makon jiya.
Gwamnan jihar Borno ya kaddamar da rukunin gidaje 100 da Dakta Muhammadu Indimi ya ginawa ‘yan gudun hijira dake garin Bama.
Gwamnatin jihar Yobe ta amince da wasu dokoki masu tsanani, ciki har da daurin rai da rai ga duk wanda aka kama da laifin fyade ga kananan yara.
Gwamnatin jihar Borno ta ce ta kebe Naira Biliyan daya don biyan ma’aikatan da suka kammala aikinsu na wa’adin shekaru 35 a jihar, da suka hada da malaman makarantun Firamare da kananan hukumomi da kuma ma’aikatan gwamnatin jihar.
Hotunan Izreal Zakari Galadima tare da Gwamnan Jihar Borno Kashim Shettima, wanda ya samu maki mafi girma a sakamakon jarabawar JAMB a shekarar 2018, da dalibai ke rubutawa kafin su samu su shiga jami'a
Bayan zanga-zangar da masu keke napep suka yi kan zargin karban na goro da kuma kuntatawa da suka ce 'yan sandan na yi musu.
Domin Kari