Jihar Naija ta bi sahun jihar Kano wajen shirin sauraron ra'ayoyin jama'a kan shirin kwaskwarima ga kundin tsarin mulkin Nijeriya.
Yau Majalisar Wakilan Dokokin jihar Kano ke zaman sauraron ra'ayin jama'a kan batun garanbawul ga kundin tsarin mulkin Nijeiya
Kasashe masu tasowa sun ce daftarin matakan rage dumamar yanayi ya kware su
Shugaban Sudan Omar el-Bashir ya ce dakatar da bincikensa da Kotun Duniya ta yi babbar nasara ce ga shi da mutanen Sudan
Yayin da sojojin kasa da kasa ke harmar ficewa daga Afghanistan, ana samun karin tashe-tashen hankula masu janyo ayar tambayar kan makomar kasar bayan ficewar sojojin kasashen duniya.
A yayin da ake kara shiga lokaci mai sarkakkiya na kusatowar zabe, wani kamfanin tsaro a Kano da Rundunar 'Yan Sandan Kano sun shirya taron bita na fayyace ma jama'a hanyoyi kare kansu.
Biyo bayan da jami'an tsaro da 'yan kato da gora da mahara suka sake kwatowa daga hannun 'yan Boko Haram yanzu kura ta fara lafawa.
Duk da ruwan sama mai tafe da sanyin watan Disamba, an cigaba da gudanar da zanga-zanga a biranen Amurka a dare na hudu a jere don nuna bacin rai kan kisan bakaken fata da ake zargin 'yan sanda fararen fata da aikatawa
Kungiyar al-Ka'ida ta reshen kasashen Larabawa ta hallaka ba-Amurken dan jarida mai daukar hoton nan Luke Somers wanda ta yi barazanar hallaka shi a 'yan kwanakin nan.
Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima ya ce da wadanda su ka kai hare hare kan bayin Allah a Borno, da maharan da ma sauran jama'a, kowa ya san cewa Allah ba fa azzalumin kowa ba ne. Sakayyar Allah ta na nan tafe.
Bayan wasu takaddamar da su ka auku kwanan nan tsakanin bangaren zartaswa da na dokoki musamman kan zargin rashin kiyaye ka'idar dimokaradiyya da kuma amfani da jami'an tsaro da hanyar da ba ta dace ba, Majalisar Dattawan Nijeriya ta bi sahun ta Wakilai wajen shirin tsige Shugaba Goodluck Jonathan.
Gwamnatin Firayim Minista Birji Rafini na Janhuriyar Nijar, wadda wasu 'yan siyasar kasar musamman 'yan adawa su ka zarga da almundahana da kuma rashin yin aiki da kundin tsarin mulkin kasa da kuma tsarin dimokaradiyya, ta tsallake rijiya da baya.
Babban sakataren majalisar dinkin duniya ya ce an samu cigaba da yaki da cutar ebola amma akwai jan aiki a gaba
Jam'iyyar PDP mai mulkin Nijeriya da babbar jam'iyyar adawa ta APC su na zargin juna da shirya ma juna gadar zare.
Ganin yadda mafarauta su ka fatattaki 'yan Boko Haram daga garuruwan Mubi da Maiha da sauran wurare a arewa maso gabashin Nijeriya, jama'a na cigaba da jinjina masu.
Allah ya ba wasu mata a Gombe sa'ar hallaka wani dan kunar bakin wake tun kafin ya sami aikata aika-aikarsa.
Ana nan ana tafka muhawara a Majalisar Dattawan Nijeriya kan bukatar Shugaba Goodluck Jonathan ta sake kafa dokar ta baci a yankin arewa maso gabashin Nijeriya. A gobe ake sa ran su ma 'yan Majalisar Wakilai za su shiga tattaunawa a kai.
Yayin da zaben 2015 ke kara karatowa, zarge-zargen yinkurin dauki-dora da bangaranci sun fara mamaye siyasar jihar.
Wani sojan Nijeriya ya ce 'yan Boko Haram din da su ka kai hari a garin Mubi na jihar Adamawa sun fi su yawan makamai da ingantattun makamai da kuma manyan makamai. Shi ya sa su ka gudu.
Rundunar tsaro a jihar Filato ta cafke wasu 'yan asalin kasar Jamhuriyar Niger akan zargin basu da takardun zama cikin kasar.
Domin Kari