A karon farko, Shugaban Majalisar Dokokin Janhuriyar Nijar da ke gudun hijira a kasar Faransa, Hamma Ahmadu ya ce ya gudu ne saboda gwamnatin kasar na kokarin kashe shi ta amfani da guba.
Wasu na hannun damarsa na tabbatar da zargin da ya yi, a yayin da kuma bangaren gwamnati ke watsi da zargin