Wani rahoton kungiyar yaki da rashawa a manyan matakai na kasashen duniya, ya nuna cewa wasu manyan kasashe ba su hana kamfanoninsu bayar da cin hanci a kasuwannin duniya, Amurka da Burtaniya ne su ka fi aiwatar da dokar.
Yayin da Najeriya ke fama da matsalar tsaro, wadda ta ke kuma shafar fannonin tattalin arziki da zamantakewa, sojojin kasar sun yi wani atisayen jiragen sama na bukin ranar samun 'yancin kai mai kama da nishadi da gargadi.
Yayin da Najeriya ke bukin zagayowa ta 60 ta ranar samun 'yancin kanta a cikin wani yanayi na matsalolin tsaro, tattalin arziki da kuma annobar COVID-19, Shugaba Buhari ya ce muddun aka hada kai za a kai ga gaci.
A cigaba da kara dora tsarin karatun allo bisa tafarkin addinin Musulunci, kamar yadda ya ke a manyan kasashen Musulmi, shawarar nan ta Mai Alfarma Sarkin Musulmi da manyan mallamai, ta a dauke ma almajirai dawainiyar bara, ta na dada samun karbuwa.
Yayin da wasu 'yan Najeriya ke yabawa da cigaba da kasancewar Najeriya dunkulalliyar kasa da sauran abuwan cigaba, wasu kuwa na ganin ba ta yi wani cigaba na kirki ba, bayan shekaru 60 da samun 'yancin kai.
Amurkawa sama da miliyan 100 ake kyautata zaton za su kalli muhawarar farko tsakanin Shugaba Donald Trump na jam'iyyar Republican da Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Joe Biden na Jam'iyyar Demokarat.
Yayin da kafafen yada labaran Najeriya ke ci gaba da yada labaran yiwuwar Minista Sadiya Umar Farouq ta auri Air Marshal Sadique, jama'ar gari kuma na ta fassara abin da hankulansu ke nuna masu.
Kasar Somaliya mai fama da rigingimun siyasa da matsalolin tsaro, ta yi sabon Firaminista, wanda ake masa kallon sabon shiga a fagen siyasa, Mohamed Hussein Roble.
Masu ruwa da tsaki na ci gaba da kokarin inganta al'amura a kasar Mali tun bayan da aka yi juyin mulki. Na baya bayan nan shi ne kokarin kawar da takunkumi a kasar ta Mali.
A ci gaba da fadi tashin samo magungunan cutar corona a Amurka, wani sanannen kamfanin harhada magunguna ya yi shelar kai wa mataki na karshe na gwajin wani magani nasa.
Ganin yadda kafafen sada zumunta ke matukar tasiri a lokacin zabe, hukumar zaben Janhuriyar Nijar da sauran masu ruwa da tsaki sun tashi haikan wajen ankarar da matasa muhimmancin amfani da kafafen yadda ya kamata.
Ganin yadda cutar corona ke barazanar sake dawowa gadan gadan musamman a sassan duniya, hukumomi a Najeriya sun shiga yin gargadi ga jama'a game da bukatar cigaba da daukar matakan kandagarki irinsu bayar da tazara da sanya takunkumin kariya.
Kasar Saudiyya ba ta kau da yiwuwar kulla dangantaka da kasar Yahudu ba, to amma ta ce sai kasar ta Isira'ila ta daidaita da Falasdinawa tukun.
A wani al'amari mai janyo takaddama da fassari iri iri, wato kotu a China ta yanke ma hamshakin mai kudin nan kuma dan siyasa, Ren Zhiqiang daurin shekaru 18 a gidan yari.
Cibiyar Yaki Da Cututtuka Masu Yado Ta Amurka ta janye wani karin bayanin da ta yi ranar Jumma'a kan yadda cutar corona ke yaduwa. Ta ce ana bukatar kara tantance bayanin.
Takaddamar da ta biyo bayan hukuncin da wata kotun Shari'ar Musulunci ta yanke ma wasu matasa a Kano na cigaba da aukuwa, ganin yadda hukumar Asusun Yara Ta Duniya (UNICEF) ta shigo, malamai kuma ke cigaba da bayani.
Nijer ta yi taron jaddada tasirinta a Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, wanda hakan ya biyo bayan rawar da ta ke takawa wajen warware matsalolin tsaro da siyasa a yankin Sahel, in ji ta.
A wani al'ami mai nuna alamar har yanzu da sauran rina a kaba game da rigimar shugabanci, siyasa da kuma matsalar tsaro, kasar ta ce ta kama wasu mutane 41 da dinbin abubuwan fashewa.
Sanadiyyar Dirowa da mahaukaciyar guguwar nan ta Sally ta yi a yankunan gabar teku musamman a jahar Alabama ta Amurka, mutane da dama sun rasa wutar lantarki baya ga wasu nau'ukan barna masu yawan gaske.
Domin Kari