Kamar yadda tsirarun jinsi su ka fi Turawa kamuwa da cutar a Amurka a bangaren manya, a bangaren matasa ma haka abin ya ke, tsirarun jinsi sun fi kamuwa.
A wani al'amari mai cike da tarihi, wasu kasashen Larabawa biyu, wato da Hadaddiyar Daular Larabawa da Bahrain, za su rattaba hannu kan yarjajjeniyar hulda da kasar Isira'ila.
A wani al'amari mai kama da tauna tsakiuwa da kuma bayar da tabbaci, rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce za ta tura manyan jami'anta don su jagoranci samar da wadataccen tsaro a zben gwamnan Edo.
Yayin da talakawan Najeriya ke yawaita kururuwar yunwa, gwamnatin kasar ta ce ta zaburo don share masu hawaye ta wajen bullo da karin tsare tsaren bayar da tallafi.
A cigaba da neman hanyoyin warware matsalolin yankin Sahel, manzon Majalisar Dinkin Duniya a Yankin na Sahel, Muhammad Ibn Chambas ya gana da Shugaba Issouhou Mahammadou na Janhuriyar Nijar.
Kamar yadda Amurkawa su ka saba kowace shekara, yau ma su na alhanin mutuwar mutane wajen 3000 a harin ta'addancin nan na ranar 11 ga watan Satumban 2001.
A cigaba da kokarin fatattakar 'yan ta'adda da ke kai hare hare a dazukan jahar Kaduna, wasu jiragen yakin sun yi ta aman wuta a wasu wuraren buyar 'ya ta'adda a dazukan jahar Kaduna.
Lauyoyin mutumin nan da ya kirkiro kafar kwarmata bayanan sirri ta Wikileaks Julian Assange, da lauyoyin gwamnatin Amurka, sun buga muhawara a wata kotun birnin London a yau dinnan Litinin.
Yanzu kasar Indiya ta zarce kasar Brazil a matsayin kasa ta biyu a duniya a yawan masu dauke da cutar corona.
A Janhuriyar Nijar, ga dukkan alamu, bangaren tsaro zai sake shiga wata rigima bayan da Hukumar Kare Hakkin Dan Adam ta zargi sojojin kasar da kare farar hula sama da 100 wadanda ba su aikata laifin komai ba.
A wani mataki na dada karkatar da tunanin matasan Janhuriyar Nijar daga miyagun ayyuka, Ofishin Jakadancin Amurka da hadin gwiwar wasu kungiyoyin kasar ta Nijar, ta karrama mafiya kwarewa a gasar amfani da kafar blog.
Wasu manyan tawagogin Amurka da Isira’ila, sun tashi daga filin jirgin saman Ben Gurion na kasar Isira’ila a yau dinnan Litinin, zuwa birnin Abu Dhabi, wanda shi ne karon farko da jirgin sama na wani kamfanin sufuri, ya tashi daga Isira’ila zuwa Hadaddiyar Daular Larabawa.
‘Yan sandan Italiya sun ce bakin haure akalla uku ne su ka mutu, shida su ka jikkata, daya kuma ya bace, bayan da karamin jirgin ruwan da ke dauke da su ya kama da wuta a tekun Ionian.
Gwamnatin Sudan da kungiyoyin ‘yan tawaye sun cimma yarjejeniyar zaman lafiya mai cike da tarihi.
Yawan masu dauke da cutar corona a Amurka ya zarce miliyan 6, baya ga yawan mace-mace dubu 183, wanda ya zarce na kowace kasa a duniya.
Idan komai ya gudana kamar yadda aka tsara, za a yi bukin rattaba hannu tsakanin Isira'ila da Hadaddiyar Daular Laraba watan gobe a birnin Washington D.C.
Domin Kari