Wannan dai wani sabon babi ne da aka bude a takaddamar da ake yi tsakanin Shekarau da abokin hamayyarsa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ya koma jam’iyyar ta PDP a watan Yuli.
“Wannan babbar barazana ce da sauyin yanayi ke haifarwa, ya kuma zama dole mu dauki wannan batu da muhimmanci, a kuma samar da matakan da za su kare aukuwar hakan.”
An bude taron koli tsakanin kasashen nahiyar Afirka da China a karo na uku wanda akalla shugabannin kasashen Afirka 40 ke halarta a birnin Beijing.
Masana tattalin arziki, na ganin China ta kasance kasa da ke zama barazana ga kasashen yammaci, wajen huldar kasuwancin da kasashen nahiyar Afirka, musamman ta fuskokin samar da ababan more rayuwa kamar wutar lantarki da fannin sufuri.
Yanzu haka, kasashen duniya da dama, sun zuba ido su ga matakin da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai dauka, bayan da wani rahoton kwamitin binciken kwakwaf na Majalisar da aka fitar a ranar Litinin ya nemi a mika batun ga kotun hukunta manyan laifuka ta ICC.
Masu sharhi a fagen wasan kwallon kafa sun yi tsokacin cewa, yanzu Emery zai fahimci irin kalubalen da ke gabansa a gasar ta Premier.
Paul Pogba da Luke Shaw sun taimakawa kungiyar Manchester United wajen lashe wasan farko a gasar Premier ta Ingila, inda ta doke Leicester City da ci 2-1.
'Yan jam'iyya mai mulki ta APC na ganin, ya kamata ya yi murabus, tun da ya bar jam'iyyar, amma 'yan PDP suka ce ba za ta sabu ba.
"In Sanar da Alummar jihar Kano cewa, Ni Hafiz Abubakar na mikawa Mai girma Gwamnan jihar Kano Takardata ta Sauka Daga Mukamin Mataimakin Gwamnan Kano."
Shugaba Trump na Amurka ya nuna shakku kan yiwuwar samun wani kyakkyawan sakamako a taron kolin da za su yi da takwaran aikinsa na Rasha Vladimir Putin a kasar Finland.
Yau aka shiga rana ta biyar a ci gaba da karawa da ake yi a gasar cin kofin duniya da Rasha ke karbar bakunci, inda tuni aka shammaci wasu manyan kasashe yayin da wasu da ba a zata suka yi zarra.
Najeriya da Croatia da ke rukunin "D" za su kara a wasanninsu na farko a ci gaba da gasar cin kofin duniya da ake yi a Rasha wacce aka fara a wannan mako.
An kafa wani babban tarihi a kasar Singapore, bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya hadu da shugaban Korea ta Arewa, Kim Jong Un domin yin taron koli da aka tsara. Trump, shi ne shugaban Amurka na farko da ke kan mulki da ya hadu da shugaban Korea ta Arewa a tarihin huldar diplomasiyyar kasashen biyu.
Shugaba Donald Trump ya bijirewa matsayar da aka cimma a taron kolin kasashen da suka fi karfin tattalin arziki na G-7 da aka kammala a Canada.
A Najeriya, ana ci gaba da cece-ku-ce- kan kalaman da tsohon shugaban kasar, Olusegun Obasanjo ya yi, na cewa gwamnatin Shugaba Buhari na kokarin ta sa a kama shi.
Kotun hukunta manyan laifuka ta ICC da ke Hauge ta wanke, tsohon mataimakin shugaban kasar Congo, Jean- Pierre Bemba daga aikata laifukan yaki da dakarun suka yi.
Wani dakarun Amurka ya rasu a Somalia, baayn da wasu 'yan bindiga suka abka masu yayin da suke taya takwarorinsu na Somalia aikin gina wani wajen tsaro
Domin Kari