Gwamnan ya tabbabarwa kungiyar cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ba su goyon baya da hadin kai su ci gaba ayyukansu, idan har za su bi tsarin dokar kasa da kudurorin gwamnati kan sha'anin tsaro.
Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta tsaida ranar soma zabukan shugabannin jam’iyyar da kuma na fidda ‘yan takarar ta, a yayin da aka tunkari babban zaben kasar na shekarar 2023.
A yayin da take shirye-shiryen soma aikin sabunta rijistar zabe, hukumar Zaben Najeriya INEC, ta bayyana fargaba kan sha’anin tsaro.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC, ta bankado wasu kamfunan hada-hadar kudade da saka hannun jari ta yanar gizo na bogi.
Rahoton hukumar bincike da kididdiga ta Najeriya, ya bayyana cewa adadin bashin da ake bin gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohin kasar ya kai naira tiriliyan 33.11 ya zuwa 31 ga watan Maris.
Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya Farfesa Charles Chukwuma Soludo ya lashe tikitin takarar zaben gwamnan jihar Anambra na jam’iyyar APGA.
Wani sabon rahoton wata hukumar Bincike ta Najeriya mai suna ‘National Social Register’ (NSR), ya bayyana cewa jihar Zamfara ce ta ke da mafi yawan mutane masu fama da talauci a Najeriya.
Akalla mutane 10 ne ‘yan gida daya, aka ba da rahoton sun mutu, sakamakon shan maganin gargajiya.
Kungiyar kwadagon Najeriya NLC, ta ce za ta koma yajin aikin da ta dakatar akan korar dimbin ma’aikata a jihar Kaduna.
An nada tsohon shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan a matsayin shugaban jami’ar Cavendish ta kasar Uganda (CUU).
Kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ta kuma sabunta dakatar da jiragen sama da fasinjoji daga Najeriya, bayan da ta ba da sanrwar dage takunkumin.
Akalla mutane 15 ne suka tsere daga hannun ‘yan bindiga masu garkuwa da su, daga cikin mutanen da aka sace a makarantar Islamiyya ta Salihu Tanko da ke garin Tegina a jihar Naija.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince a hau teburin sasantawa da 'yan kabilar Igbo, da ma duk wadanda ke fafutukar ballewa da raba kasar.
Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya yi kira ga shugaban Najeriya Muhammadu da kada ya kauracewa nauyin da kundin tsarin mulkin kasa ya dora masa a matsayin kwamandan askarawan Najeriya, a sha’anin yaki da kalubalen tsaro a kasar.
Najeriya ta yi asarar zunzurutun kudi har dalar Amurka biliyan 40.6 a shekarar 2020 sakamakon kalubalen tsaro, a yayin da ayukan kungiyar Boko Haram, ISWAP da ‘yan bindigar daji suka addabi kasar.
Kungiyar Boko Haram ta tabbatar da mutuwar shugabanta Abubakar Shekau, ta hanyar wani hoton bidiyo da ke nuna sabon shugaban kungiyar, wanda ya sha alwashin daukar fansa akan kisan da aka yi wa shugaban na su.
Gwamnatin jihar Anambra da ke kudancin Najeriya ta musanta rade-radin da ake bazawa, na cewa an dawo da rusasshiyar kungiyar na ta tsagerun ‘yan banga da aka fi sani da ‘Bakassi Boys’, domin taimakawa wajen yaki da matsalar tsaro a yankin Kudu maso Gabas.
Gwamnatin jihar Benue ta ayyana ranakun Alhamis da Juma’a na kowane sati a cikin watannin Yuni da Yuli, a matsayin ranakun hutu ga ma’aikatan gwamnati, domin baiwa ma’aikatan damar fuskantar aikin gona.
Hukumar zaben Najeriya, INEC, ta bayyana ranakun da za’a gudanar da zabukan gwamna a jihohin Ekiti da Osun, da ke kudancin kasar, a yayin da kuma ta ba da sanarwar kirkiro sababbin rumfunan zabe a fadin kasar.
Sai dai duk da haka, Bawa ya ce wadannan barazanar ba za su tsorata su ba, inda ya lashi takobin cewa hukumar za ta ci gaba da aikinta.
Domin Kari