Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kada Ka Kauracewa Nauyin Kundin Tsarin Mulki - Tambuwal Ya Gargadi Buhari


Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal.

Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya yi kira ga shugaban Najeriya Muhammadu da kada ya kauracewa nauyin da kundin tsarin mulkin kasa ya dora masa a matsayin kwamandan askarawan Najeriya, a sha’anin yaki da kalubalen tsaro a kasar.

A yayin da yake jawabi ga kungiyoyin matasa a karkashin inuwar majalisar matasa ta kasa a Sokoto, Gwamna Tambuwal ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya ya dora nauyin sha’anin tsaro ne kacokam akan gwamnatin tarayya.

Tambuwal yana mai da martani ne akan wata sanarwa da aka danganta da shugaban kasar, wanda ya zargi gwamnonin jihohi akan matsalolin tsaro da ake samu a jihohinsu.

Shugaban Kasar Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Kasar Najeriya Muhammadu Buhari

Mai magana da yawun shugaban kasa Garba Shehu ne ya fitar da sanarwar, wadda ta zargi gwamnonin jihohi da kasawa wajen samar da tsaro a jihohuinsu, a yayin mai da martani akan wata matsaya da gwamnonin jam'iyyar PDP suka cimmawa.

Gwamna Tambuwal ya ce a matsayin sa na gwamna, idan ya ba da umarni kai tsaye ga kwamandan soji, ko daraktan hukumar tsaro ta SSS, ko ma duk wani shugaba na hukumar tsaro a jiharsa, bisa tsarin da ake kai a halin yanzu ba za su bi ba har sai sun sami izni daga manyansu a Abuja.

Karin bayani akan: Shugaban Kasa da Gwamnonin, Majalisar Wakilai, Majalisar Dattawa, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

Ya ce su kuma shugabannin na su da ke Abuja din, dole ne sai sun tuntubi shugaban kasa, wanda shi ne babban kwamandan askarawan Najeriya, kamar yadda kundin tsarin mulki ya yi tanadi.

Shugaba Najeriya Muhammadu Buhari Da Shugabannin Jami'an Tsaron Kasa
Shugaba Najeriya Muhammadu Buhari Da Shugabannin Jami'an Tsaron Kasa

Tambuwal ya ce kamata ya yi shugaban kasa ya fuskanci hanyoyin magance matsalar tsaro, su kuma a bangarensu na gwamnoni, a shirye suke da su mara masa baya akan duk wani kokari da gwamnatin tarayya ke yi wajen tabbatar da tsaro a kasar.

Ya ce Najeriya muhimmiyar kasa ce da bai kamata a zubar da kimar ta ba, yana mai nuni da cewa akwai bukatar zama lafiya da hadin kai, ta yadda za’a amfana da karfin dimbin matasa da kasar take da su.

Gwamnan ya kara da cewa wannan ne ya sa gwamnatinsa ta dukufa wajen saka jari a bangaren ilmi da aikin gona, ta yadda za’a baiwa matasa damar kasancewa ‘yan kasa na gari da za su amfani kan su, su kuma amfani al’umma baki daya.

To sai dai kuma ya bayyana damuwa da yadda dukan wadannan bangarorin biyu suke fuskantar kalubale, sakamakon rashin isassun kudade da matsalar tsaro.

XS
SM
MD
LG