Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 15 Daga cikin Wadanda Aka Sace A Tegina Sun Tsere Daga Hannun 'Yan Bindiga.


Akalla mutane 15 ne suka tsere daga hannun ‘yan bindiga masu garkuwa da su, daga cikin mutanen da aka sace a makarantar Islamiyya ta Salihu Tanko da ke garin Tegina a jihar Naija.

Wadanda suka tsere din suna daga cikin manyan mutanen da ‘yan bindigar suka sace tare da daliban makarantar ta Salihu Tanko 156 a karshen watan Mayun da ya gabata.

Rahotanni sun bayyana cewa bayan sace mutanen, ‘yan bindigar sun ware manyan mutanen daga yara, inda suka kai su a dajin Zamfara, yayin da su kuma yaran aka boye su a wani wurin da ba kai ga ganowa ba.

Mutanen sun sami kubuta ne ta hanyar balle kyauren kofar gidan da aka kulle su a cikin jeji, bayan bacci mai nauyi ya kwashe wadanda ke tsare da su sakamakon mayen barasa.

Daya daga cikin mutanen da suka arce din ya sami isa garin Tegina inda ya ba da labarin, yana mai cewa bayan fitowar ta su, sun rarrabu ne suka gudu ta bangarori daban-daban, don gudun kada su ja hankalin wasu ‘yan bindigar da ke cikin jejin..

Yanzu haka kuma gwamnatin jihar Naija ta shiga aikin neman sauran mutanen, domin taimaka musu dawowa gida, inda kuma aka sami gano karin mutane 3 da yammacin Lahadi.

Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello (Hoto: Twitter, Gwamnatin jihar Neja)
Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello (Hoto: Twitter, Gwamnatin jihar Neja)

Wani jami’in gwamnatin jihar ya shaidawa manema labarai cewa yanzu haka wadanda suka sami kubutowa din suna samun kulawar likitoci, a yayin da kuma aka ba su abinci da sababbin tufafi. Ya ce ba da dadewa ba za’a sada su da iyalansu.

Wasu majiyoyi kuma sun bayyana cewa yanzu haka an tura jami’ai a titin Tegina zuwa Birnin Gwari, domin jiran isowar sauran mutane 10 da suka sami kubuta.

Majiyar ta ce da zara an same su, za’a wuce da su zuwa Minna inda za’a duba lafiyarsu, kafin hannunta su ga iyalansu.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin rahotannin ke bayyana cewa ana ci gaba da artabu tsakanin dakarun sojin Najeriya da ‘yan bindigar da suka sace daliban makarantar kwalejin gwamnatin tarayya ta Yawuri a jihar Kebbi.

Wasu daga cikin daliban da suka tsira daga hain 'yan bindigar a jihar Kebbi
Wasu daga cikin daliban da suka tsira daga hain 'yan bindigar a jihar Kebbi

Kamar yadda rahotannin suka bayyana, dakarun na Najeriya dai sun yi wa ‘yan bindigar kofar rago ne, inda suka sami kashe da dama daga cikin su, yayin da kuma suka sami ceto dalibai kusan 10 da malamai 2.

XS
SM
MD
LG