Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Kwadagon Najeriya Za Ta Koma Yajin Aiki Na Kasa Baki Daya Kan Korar Ma'aikatan Jihar Kaduna


KADUNA: Kungiyar kwadago ta yi zanga zanga.
KADUNA: Kungiyar kwadago ta yi zanga zanga.

Kungiyar kwadagon Najeriya NLC, ta ce za ta koma yajin aikin da ta dakatar akan korar dimbin ma’aikata a jihar Kaduna.

A wani taron shugabanninta da ta gudanar da yammacin ranar Talata, kungiyar kwadagon Najeriya ta yi matsayar sake tsunduma yajin aiki, wannan lokacin na kasa baki daya, domin abin da ta kira kasawar gwamnatin jihar ta Kaduna, na mutunta yarjejeniyar da aka cimma akan lamarin.

Shugaban kungiyar kwadagon Kwamared Ayuba Wabba ya ce sun yi iya bakin kokarinsu na ganin gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya aiwatar da jarjejeniyar da aka cimma a zaman sulhun da gwamnatin tarayya ta jagoranta, amma lamarin ya ci tura.

Shugaban kungiyar kwadagon Najeriya ta NLC, Ayuba Wabba yana jawabi a wajen zanga-zangar (Twitter/NLC)
Shugaban kungiyar kwadagon Najeriya ta NLC, Ayuba Wabba yana jawabi a wajen zanga-zangar (Twitter/NLC)

Ya kara da cewa kungiyar ta kuma aike da wasiku zuwa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da Ministan kwadago Chris Ngige, inda ta fadakar da su akan kin mutunta yarjejeniyar da gwamnatin jihar Kaduna ta yi.

Wabba ya ce kungiyar ta yanke shawarar sake komawa yajin aikin ne bayan duk wasu hanyiyo da ta bi na ganin an daidaita lamari sun tashi a tutar babu.

Akan haka ya ce kungiyar ta sanar da dukan hukumomin gwamnati, haka kuma ta umarci dukan kungiyoyin ma’aikata da ke karkashinta da su soma kimtsa ma’aikata domin soma yajin aikin.

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai
Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai

Shugaban kwadagon ya zargi gwamnatin ta jihar kaduna da take tanade-tanaden doka, inda ya ce “gwamna Nasir El-Rufai yana mulki irin na soja ne ba mulkin dimokaradiyya ba.”

A ranar 17 ga watan Mayu ne kungiyar kwadagon ta shiga yajin aikin gargadi na kwanaki 5, akan korar dubban ma’aikata a jihar ta Kaduna.

Zaman sasanta rikicin kungiyar kwadago ta NLC da gwamnatin jihar Kaduna
Zaman sasanta rikicin kungiyar kwadago ta NLC da gwamnatin jihar Kaduna

To sai dai ta janye yajin aikin bayan kwanaki 3, biyo bayan sa bakin gwamnatin tarayya, wacce ta jagoranci zaman sasantawa har aka rattaba hannu akan yarjejeniyar sulhu tsakanin kungiyar kwadagon da gwamnatin jihar Kaduna.

XS
SM
MD
LG