Rikicin Boko Haram ya mayar da dubban yara a arewa maso gabashin Najeriya marayu. Akasarin yaran su na fuskantar kalubale na rayuwa sosai. Amma wasu daga cikinsu, sun samu rayuwa mai kyau a jihar Sokoto, Haruna Shehu Marabar Jos ya ziyarci wata makaranta da ake kula da irin wadannan yara a Sokoton.
No media source currently available
A lokacin babbar sallah, Musulmai a fadin duniya suna yin hadaya, wato yanka dabbobi domin yin sadaka domin neman lada daga wurin Allah. Wasu ma’aikatan Sashin Hausa na Muryar Amurka sun yi takakkiya zuwa Pennsylvania domin gabatar da wannan ibada.
Labarin zababben kansila da ya rungumi sana’ar sayar da shayi a Kano, wanda ya ke karfafa gwiwar sauran matasa da kar su rika raina sana’ar yi.
Al'ummomi a Najeriya sun fara daukan matakan kare unguwanninsu daga masu garkuwa da mutane da suka addabe su da satar mutane domin neman kudin fansa.
Shugabar hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Borno, Hajiya Yabawa Kolo ta ce gwamnatin jihar ta na iya bakin kokarinta wajen kyautata rayuwar ‘yan gudun hijirar rikicin Boko Haram.
Shugaban kasar Nijar, Mohamed Bazoum a hira ta musanman da Muryar Amurka ya ce matsalar tsaro ce babban kalubalen da ya fuskanta tun da ya zama shugaban kasa watanni bakwai da suka wuce.
Bayan shekara hudu, hukumomi a yankin Tillaberi na Jamhuriyar Nijar, sun dage dokar hana aiki da babura da aka sanya a wani bangare na yaki da ayyukan ‘yan bindiga. Tuni dai masu sana’ar acaba da masu gyaran babura suka fara nuna farin ciki da dage dokar da aka yi. Rahoton Yusuf Abdoulaye, Niamey.
Bikin Lasar Gishiri, dadaddiyar ala’ada ce da Fulanin yankin Agadez suka jima suna yi a kowacce shekara.
A Najeriya alamu na nuna cewa jama'a sun fara debe tsoron ‘yan ta'adda domin suna bayar da gudunmuwa wajen kamawa ko kisan barayin, wanda kuma bai rasa nasaba da ganin cewa hukuma ta kasa magance matsalolin.
Sanata Shehu Sani ya yi bayanin yadda jirgin kasan da su ka shiga zuwa Abuja ya sha da kyar bayan harin 'yan-bindigan da ya ce ya lalata hanyar dogon a tsakanin Rijana da Dutse. Saurari rahoton Isah Lawal Ikara