Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Tsaron Somaliya Sun Yi Nasarar Kashe Mayakan Al-Shabab Da Suka Kai Hari Wani Otel


Harın Otel a Somalia
Harın Otel a Somalia

Jami'an tsaron Somaliya a ranar Laraba sun kawo karshen wani harin da ya dau sa'o'i 24 a wani Otel da ke tsakiyar birnin Beledwyne, wanda ya yi sanadin mutuwar mutanen da ba a san adadinsu ba, ciki har da daukacin 'yan ta'addar Al-Shabab da suka kaddamar da harin, in ji jami'ai

An fara kai harin ne a ranar Talatar da ta gabata, inda wata mota shake da bama-bamai ta tarwatse a Otel din Alkhahira, wanda ya ke mazaunin dattijan gargajiya da jami'an soji da ke da ruwa da tsaki wajen hada kai da gwamnatin kasar a yakin da ake yi da al-Shabab.

Otel a Somali inda aka kai hari
Otel a Somali inda aka kai hari

Magajin garin Beledweyne, Omar Alasow, a ranar Laraba ya ce jami’an tsaro “sun yi nasarar kawo karshen harin” kuma mayakan al-Shabab shida sun mutu. Amma har yanzu dai ba a san adadin fararen hula da aka kashe a harin ba.

Kungiyar al-Shabab mai alaka da al-Qaida ta dauki alhakin kai harin.

Baledweyne mai tazarar kilomita 335 (kilomita 208) arewa da Mogadishu babban birnin kasar, shi ne babban birnin yankin Hiran, kuma wuri mai muhimmanci a yakin da ake yi da kungiyar ta al-Shabab.

Kiyasin adadin wadanda suka mutu sakamakon harin ya banbanta. Wani mazaunin yankin mai suna Muhsin Abdullahi ya ce an kashe mutane shida da suka hada da wasu fitattun dattawan gargajiya biyu. Sai dai wani shaida, Hussein Jeelle Raage, ya ce uku daga cikin iyalansa na cikin akalla mutane 11 da ya san sun mutu.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG