Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Margaret Thatcher Ta Rasu


Tsohuwar firayim ministar Britaniya, Margaret Thatcher, wadda ta rasu litinin, 8 Afrilu, 2013

Tsohuwar firayim ministar, wadda ake kira Mace mai kamar maza, ita ce macen farko da ta taba rike kujerar a tarihin Britaniya.

Tsohuwar firayim ministar Britaniya, Margaret Thatcher, ta mutu tana da shekaru 87 da haihuwa, a bayan da ta samu toshewar jijiyar jini.

Kakakin iyalinta, Lord Tim Bell, yace mace kwaya daya tak da ta taba rike mukamin firayim ministar Britaniya ta rasu yau litinin da safe. Mintoci kadan bayan samun labarin mutuwarta, jama’a sun fara zuwa su na ajiye furanni da sakonnin ta’aziyya a kofar gidanta a London.

Firayim minista David Cameron, ya tsinke ziyarar da yake yi a Spain da Faransa bayan samun wannan labarin. Ya ce kasarsa ta yi rashin "gwarzuwar shugaba, gagarumar firayim minista, kuma ‘yar kasa.”

Margaret Thatcher, wadda aka sani da kaifin magana, ta jagoranci jam’iyyar Conservative ta lashe zabe har sau uku daga 1979 zuwa 1990. Rabon da a samu wani firayim ministan da yayi mulki na tsawon wannan lokaci ba tare da yankewa ba a kasar ta Britaniya tun cikin karni na 19.

Mrs. Thatcher, wadda ake ma lakabi da sunan “Iron Lady” ko mace mai kamar maza a saboda jarumtakar siyasarta, mai ra’ayin rikau ce sosai wadda ta karya lagon kungiyoyin kwadago na kasar Britaniya, ta kawar da mafi yawan sassaucin farashin da gwamnati keyi, ta kuma kara karfin irin rawar da kamfanoni masu zaman kansu ke takawa.

Ta jagoranci Britaniya a yakin da ta yi da Ajantina kan tsibiran Falklands a 1982, ta yi adawa sosai da hada kan kasashen Turai karkashin inuwar tarayya guda, sannan ta kulla abinda ta kira “dantaka ta musamman” ta kut da kut da shugaban Amurka Ronald Reagan wadda ta taimaka wajen gaggauta faduwar kwaminisanci da rushewar Tarayyar Soviet.
XS
SM
MD
LG