Accessibility links

Ma'aikatan Wutar Lantarki Sun Fara Kauracewa Aiki


Wani ma'aikacin kamfanin lantarki na Najeriya yana gyaran waya a Lagos, Yuli, 2011.

Ma'aikatan wutar lantarkin sun lashi takobin tsinke wutar lantarki idan har ba a biya su hakkokinsu kafin a mika harkar wutar ga kamfanoni masu zaman kansu ba

Ma'aikatan wutar lantarki a Najeriya sun fara kauracewa ofisoshinsu domin su nuna rashin jin dadinsu kan yadda har yanzu ba a biya su kudadensu na sallama daga aiki ba, yayin da gwamnatin Najeriya take kokarin mika harkar wutar lantarki da dukkan kadarorinsu ga kamfanoni masu zaman kansu da suka saye su.

Ana hasashen cewa da yawa daga cikin wadannan ma'aikata zasu rasa ayyukansu idan harkar samar da wutar lantarkin ta koma hannun 'yan kasuwa.

Sakataren kungiyar ma'aikatan wutar lantarki na yanki mai klula da jihohin Sokoto, Zamfara da Kebbi, Comrade Yusuf Ahmed Abdulkarim, ya fadawa wakilin Muryar Amurka, Myrtala Faruk Sanyinna, cewa babu gaskiya a cikin ikirarin da gwamnatin Najeriya ta yi cewar ta biya ma'aikatan PHCN kudadensu na sallama.

Yace ko sisin kwabo ba a biya su ba.

Comrade Yusuf, ya kuma ce, ba a shiyyar Sokoto kawai aka fara wannan kauracewa wuraren aiki ba, a duk Najeriya ne ake gudanar da wannan gangamin. Matakin da zasu dauka na gaba in ji shi, shi ne katse wutar lantarkin bakii daya a duk fadin Najeriya.

Ga cikakken bayani a wannan rahoto da Murtala Faruk Sanyinna ya aiko daga Sokoto.
XS
SM
MD
LG