Accessibility links

Kungiyar Ansaru Ta Saki Bidiyo Na Bafaranshe Da Ta Kama

  • Garba Suleiman

Wani hoton da 'yan kungiyar Ansaru suka bayar a watan Disambar 2012. Kungiyar ta fito da bidiyo na wani bafaranshe da ta sace.

An ga Francis Collomp da aka sace a watan Disamba yana rokon gwamnatocin Faransa da Najeriya da su taimaka a sako shi.

Kungiyar nan ta Jama'atu Ansarul Muslimina Fi Biladis Sudan, wadda aka fi sani da sunan Ansaru, ta sako faifan bidiyo na wani dan kasar Faransa mai suna Francis Collomp wanda ta sace ta ke garkuwa da shi tun cikin watan Disamba.

An ji shi a cikin bidiyon yana rokon da a tattauna da kungiyar domin a sako shi.

Kungiyar Ansaru, wadda sunanta yake nufin "Kungiyar Kare Musulmi a Kasashen Bakar Fata", ta fara kunno a watan Janairun 2012, kuma ana kyautata zaton cewa tana da alaka da kungiyar Boko haram.

Kungiyar ta Ansaru ta sace ko kuma ta kashe 'yan kasashen waje da dama a yankin arewacin Najeriya tun bullowarta.

Ana dora wa kungiyar Ansaru laifin sace wani dan Ingila da wani dan kasar Italiya a shekarar 2011. A watan Fabrairu, ta dauki alhakin kashe wasu 'yan kasashen waje su 7 dake aiki a wani kamfanin kwangilar gina hanya a Jihar Bauchi a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Shi dai wannan Bafaranshe Collomp, an sace shi ne daga gidansa dake Rimi a Jihar Katsina, a watan Disambar bara. Yana aiki ma kamfanin Vergnet mai samar da wutar lantarki ta sabbin hanyoyin zamani, wanda kuma ke aikin gina masana'antar samar da wutar lantarki daga iska ta farko a Najeriya.

An ce gwamnatin Faransa tana nazarin wannan bidiyo domi n tantance sahihancinsa.
XS
SM
MD
LG