Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Yobe Ta Yi Tur Da Harin Ta'addanci Na Gujba


Wani mutum da yaji rauni a harin da aka kai kan wata kwaleji da ake kyautata zaton mayakan kishin Islama suka kai, yana kwance a cikin motar asibiti a asibitin gwamnatin tarayya dake Nguru jihar Yobe. Satumba 30, 2013.
Wani mutum da yaji rauni a harin da aka kai kan wata kwaleji da ake kyautata zaton mayakan kishin Islama suka kai, yana kwance a cikin motar asibiti a asibitin gwamnatin tarayya dake Nguru jihar Yobe. Satumba 30, 2013.

Kakakin gwamnan yace wannan harin, aikin ta'addanci ne abin kyama, yana mai rokon da Allah Ya tona asirin wadanda suka kai shi

Gwamnatin jihar Yobe ta yi Allah wadarai da farmakin da wasu 'yan bindigar da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne suka kai a kan kolejin koyon aikin gona ta jihar dake Gujba, tana mai bayyana wannan harin a zaman ta'addanci, abin kyama.

Kakakin gwamna Ibrahim Gaidam na Jihar Yobe, Malam Abdullahi Bego, yace gwamnan ya kuma roki Allah da Ya tona asirin wadannan marasa imani da suka samu dalibai su na cikin barcinsu suka far musu su na karkashe su.

Abdullahi Bego yace duk wadanda suka kai wannan harin zasu gamu da fushin hukuma in sun shiga hannu, haka kuma tabbas su na rokon Allah da Ya hukumta wadannan marasa imanin dake kashe mutane babu gaira babu dalili, su na hana jama'ar kasa jin sakat a saboda bahaguwar manufarsu.

Yace su na kokarin ba jami'an tsaro irin hadin kan da suke bukata, kuma su na rokon jama'a da su ci gaba da bayyanawa hukumomin tsaro duk abinda suka gani bambarakwai domin a samu sukunin maganin wadannan 'yan ta'adda.

Gwamna Ibrahim Geidam ya kai ziyara asibitin Damaturu inda ya jajantawa wadanda suka ji rauni.

Ga tattaunawar da Abdullahi Bego yayi da Sahabo Imam Aliyu...

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:33 0:00
Shiga Kai Tsaye
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG